--
Fitaccen fasto ya rasu, ya bukaci a birnesa da katon talabijin (Hotuna)

Fitaccen fasto ya rasu, ya bukaci a birnesa da katon talabijin (Hotuna)


Shahararren faston nan na kasar Uganda mai suna Augustine Yiga ya kwanta dama - Ya rasu ne watanni kadan bayan an kama shi da laifin yada jita-jita a kan COVID-19 


Faston ya rasu ne sakamakon fama da yayi da ciwon hanta Augustine Yiga, shararren faston nan na Uganda ya mutu, Jaridar The nation ta wallafa. Faston ya rasu ne bayan watanni 5 da kama shi da laifin yayata cewa Coronavirus zazzabi ne wanda dama aka dade ana yinsa. 




Faston cocin Revival da ke Kawaala, a Kampala, wanda aka fi sani da Abizaayo, ya rasu ne a ranar 26 ga watan Oktoba, a asibitin Nsambya inda aka kwantar dashi sakamakon fama da ciwon hanta. An kawo gawarsa cocin a ranar Asabar, 31 ga watan Oktoba da rana. Za'a rufeshi ranar Lahadi kusa da mahaifiyarsa. 


Kamar yadda ya bayar da wasiyya, ya na so a wuni ana nuna burniyarsa a gidan talabijin na ABS. Mutuwarsa ta zo bayan watanni 5 da kama shi da yada labaran bogi da jita-jita a kan COVID- 19. A satin da ya gabata, 


wasu mutane a kafafen sada zumuntar zamani suka yi ta yada labarin mutuwarsa, amma daga baya iyalinsa suka karyata labarin, inda suka ce yana nan da ransa. Dansa, Andrew Jjengo yace faston ya dade bashi da lafiya. 


SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Fitaccen fasto ya rasu, ya bukaci a birnesa da katon talabijin (Hotuna) "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?