
Firaministan Isra'ila ya tafi Saudiyya don ganawar sirri da yarima mai jiran gado
Kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun ce Firaminista Benjamin Netanyahu, ya tafi Saudiyya a asirce a ranar Lahadi don gana wa da Yarima Mohammed bin Salman mai jiran gado da kuma sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo.
Wasu bayanan bin diddigin zirga-zirgar jiragen sama sun nuna wani jirgin da Mista Netanyahu ke amfani da shi ya tafi birnin Neom, inda a can shi da yariman da Mista Pompeo suka tattaunawa.
Sai dai babu tabbacin hakan a hukumance.
An kuma bayyana cewa taron ya ƙunshi har da shugaban hukumar leƙen asirin Isra'ila da cikin tawagar.
A cikin wani bayani a Twitter, daga daga cikin masu ba Netanyahu shawara ya nuna cewa ziyarar ta faru ba tare da bayar da tabbaci a hukumance ba
Ganawar ita ce irinta ta farko tsakanin shugabannin ƙasashen da suke da daɗaɗɗen tarihin gaba da juna, waɗanda a yanzu Amurka ke son shirya su.
A baya-bayan nan ne Shugaba Trump ya jagoranci sasanta tsakanin Isra'ila da ƙasasehn UAE da Bahrain da Sudan.
Saudiyya ta yi taka tsan-tsan wajen yin maraba da lamarin, amma ta nuna cewa ba za ta bi sahu ba har sau an cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Sira;ila da Falasɗinawa.
A yanzu dai gwamnatin Trump na son janyo ra'ayin Saudiyya ta shirya da Isra'ila.
SOURCE: BBCHAUSA
0 Response to "Firaministan Isra'ila ya tafi Saudiyya don ganawar sirri da yarima mai jiran gado"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?