--
EndSARS: Yadda rikici ya ɓarke tsakanin gwamnatin Buhari da gidan talbijin na CNN

EndSARS: Yadda rikici ya ɓarke tsakanin gwamnatin Buhari da gidan talbijin na CNN


Duk da koke da kuma barazanar da gwamnatin Najeriya ta yi wa gidan talabijin na CNN da ke Amurka, sai da kafar ta sake fitar da bidiyon bincike game da zanga-zangar EndSARS a kasar.


Karo na biyu kenan da CNN ke wallafa bincike da ke ikirarin tabbatar da cewa sojojin Najeriya sun yi harbi a kan masu zanga-zangar EndSARS a Lekki Toll Gate da ke Jihar Legas ranar 20 ga watan Oktoba.


Bidiyon farko da aka wallafa ranar 18 ga Nuwamba ya nuna yadda aka harbi wasu daga cikin 'yan zanga-zangar bayan tattara bayanai daga mutum kusan 100 da kuma hotuna da bidiyon da aka wallafa a shafukan zumunta.


Binciken na CNN ya nuna cewa harsasan bindigar da sojoji suka yi amfani da su masu kisa ne kuma an sayo wasu daga cikinsu daga ƙasar Serbia a shekarun baya, saɓanin abin da rundunar sojan ta bayyana cewa harsasan ba masu kisa ba ne.


Wani bidiyon kyamarar tsaro ta CCTV kuma da CNN ɗin ta wallafa ranar Talata, wanda ta ce na wani gini ne da ke kallon Toll Gate ɗin na Legas, ya nuna ƙarin bayani fiye da yadda sojoiji suka yi.


Kafar talabijin ɗin ta ce binciken nata ya tabbatar da mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu da dama.


Martanin gwamnatin Najeriya:


Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani iri-iri ga binciken na CNN kuma na baya-bayan nan shi ne wanda Ministan Yaɗa Labarai da Al'adu Lai Mohammed ya ce duk abin da aka nuna "maimaici ne domin mun gan shi a baya".


Da yake magana a wani shirin talabijin na NTA, ministan ya ce har yanzu CNN ba ta fito da hujja ba ƙarara kamar gawarwakin mutanen.


"CNN ta matsu ne kawai, wannan fim ɗin da muka gani babu komai a cikinsa illa maimaicin abin da muka saba ji na labaran ƙarya.


"Abin da muke tamabayar CNN shi ne; ina hujja, ina gawarwakin. Sojoji sun sha nanatawa cewa sun je Toll Gate sun harba harsasai marasa kisa kuma har yanzu CNN ba ta iya kawo abin da ya ci karo da wannan bayani ba."


Tun farko ministan ya bayyana cewa: "Wannan babban abu ne kuma ya kamata a hukunta CNN."


Cikin wata wasiƙa da ministan ya aike wa gidan talabijin ɗin, Lai Mohammed ya ce CNN ta karya ƙa'idojin aikin jarida saboda "ba ta tuntuɓi ko mutum ɗaya ba daga cikin jami'an gwamnatin Najeriya". CNN ta ce ta tuntuɓi rundunar sojan Najeriya da gwamnatin Legas kafin wallafa binnciken.


Abin da CNN ta binciko


Dakarun Barikin Bonny da ke Jihar ta Legas ne suka isa wurin zanga-zangar da misalin ƙarfe 6:29 ranar 20 ga watan Oktoba, a cewar CNN. Saia dai da farko sojojin sun haƙiƙance cewa ba su je wurin ba kafin daga bisani su yarda cewa sun je.




 Binciken ya nuna cewa harsasan bindigar da sojojin suka yi amfani da su masu kisa ne kuma an sayo wasu daga cikinsu daga ƙasar Serbia a shekarun baya, saɓanin abin da rundunar sojan ta bayyana cewa harsasan ba masu kisa ba ne.


"Ya zuwa ƙarfe 6:43 sai aka fara jin ƙarar harbin bindiga," in ji rahoton. Kazalika, wasu sun faɗa wa CNN cewa 'yan sanda ma sun je wurin kuma sun buɗe wuta.


Haka nan, wani bidiyon kyamarar tsaro ta CCTV da CNN ta ce ta samu, kafin a gabatar da shi gaban kwamitin shari'a da ke bincike kan lamarin, bai nuna sanda sojojin ke harbi kan mutane ba.


Da farko sojoji sun ƙaryata zuwansu wurin kwatakwata


Tun bayan da aka fara yaɗa labarin cewa an ga sojoji na harbi a Lekki Toll Gate, rundunar sojan Najeriya ba ta yi wata-wata ba ta ce labarin ƙarya ne.


Haka aka ci gaba da tafiya har zuwa lokacin da Gwamnan Legas Sanwo-Olu ya faɗa cewa sojoji sun kira shi sun yi masa tayin fitowa kan tituna idan yana buƙata, amma bai ce ya yarda ba ko kuma a'a.


Bayan fara zaman kwamitin shari'ar ne kuma Birgediya Janar Ahmed Taiwo ya faɗa masa cewa Sanwo-Olu ne ya nemi sojojin su kai ɗauki "bayan zanga-zangar ta rikiɗe zuwa tashin hankali" sannan kuma ba su yi harbi kan masu zanga-zangar ba.


Gwamna Sanwo-Olu ya musanta cewa shi ne ya gayyaci sojojin yayin wani zaman kwamitin, abin da sojojin suka bayyana da cewa "abin takaici da rashin jin daɗi".


Daga baya kuma rundunar ta tabbatar cewa dakarunta sun je wurin kuma sun yi harbi amma ba da harsashi mai kisa ba.




 

Binciken na shan yabo da suka daga 'yan Najeriya musamman a shafukan sada zumunta. 


Wani ƙarin abin da ya ja hankalinsu shi ne yadda wata wakiliyar BBC ta bayyana kai-tsaye a kafar talabijin cewa ba ta ga wani wanda aka harba ba a lokacin da take wurin da abin yake faruwa. 


 Saboda haka ne masu goyon bayan gwamnati da ke da ra'ayin cewa lamarin ya faru, ke yabon CNN, waɗanda ke ganin bai faru ba kuma ke yabon BBC.


SOURCE: BBC HAUSA

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "EndSARS: Yadda rikici ya ɓarke tsakanin gwamnatin Buhari da gidan talbijin na CNN"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?