
EndSARS: Ba za mu tilasta wa kowani jami’in dan sanda komawa bakin aiki ba –Hukumar yan sanda
Hukumar yan sanda ta yi martani a kan rahoton cewa tana shirin sallamar jami'anta da suka ki komawa bakin aiki bayan zanga-zangar EndSARS - PSC ta bayyana hakan a matsayin karya inda tace ba za ta tilasta wa jami'anta dawowa aiki ba
Sai dai ta ce abu guda da za ta iya yi shine ta lallashe su domin suna cikin juyayin rashi da suka yi a yanzu Hukumar yan sandan Najeriya ta bayyana cewa ba za ta tursasa ma kowani jami’in dan sanda komawa bakin aiki ba,
jaridar Premium Times ta ruwaito. Hukumar PSC din ta bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 1 ga watan Nuwamba, a cikin wata sanarwa daga Shugaban harkokin labaranta da hulda da jama’a, Ikechukwu Ani.
Jawabin martani ne ga wata wallafar jarida wacca ta bayyana cewa hukumar ta yi barazanar korar duk jami’an da suka ki dawowa bakin aiki.
Hukumar ta ce rahoton kanzon kurege ne, cewa zai zama rashin hankali tsantsa ga hukumar idan ta kori kowani dan sandan da ya ki komawa aiki.
A baya dai mun ji yadda zanga-zanga a sassa daban-daban na kasar ya koma rikici bayan sojoji sun harbi masu zanga-zangar lumana a Lekki toll gate da ke jihar Lagas. Tuni dai yan sanda da dama suka yi watsi da ayyukansu bayan barkewar rikicin.
A cikin jawabin Mista Ani, ya ce abunda kawai hukumar za ta iya yi shine ta roki jami’an yan sanda su koma bakin aiki duba ga yawan rayukan da yan sandan suka rasa a yayin zanga-zangar.
Ya kuma bayyana cewa hukumar na cikin halin juyayi don haka rahoton barazanar korar zai zama rashin hankali.
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "EndSARS: Ba za mu tilasta wa kowani jami’in dan sanda komawa bakin aiki ba –Hukumar yan sanda "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?