--
Duba hanyoyi guda 7 na Yadda za a duba sakamakon jarrabar WAEC ta 2020

Duba hanyoyi guda 7 na Yadda za a duba sakamakon jarrabar WAEC ta 2020


Hukumar WAEC ta sanar da sakin sakamakon jarabawar daliban da suka zauna a wannan shekarar - Kamar yadda shugaban hukumar na Najeriya ya sanar, kashi 65.24 sun samu nasara har a darussan Lissafi da Turanci 


Ya kara da cewa, kashi 13.98 wanda yayi daidai da dalibai 215,149 ne aka rike wa sakamakonsu Hukumar shirya jarrabawar kammala makarantar sakandire ta kasashen Afrika na yamma (WAEC) ta saki sakamakon jarrabawar shaidar kammala sakandire (SSCE) na shekarar 2020. 


Tun ranar Lahadi WAEC ta yi alkawarin cewa za ta saki sakamakon jarrabawar ranar Litinin, 2 ga watan Nuwamba. Matakan duba sakamakon jarrabawar basu da wahalar fahimta ga duk dalibin da zai duba sakamakonsa. 


Dalibi yana bukatar katin shaidar rubuta jarrabawa mai dauke da wasu muhiman lambobi, ana bukatar wadannan lambobi domin duba sakamakon jarrabawar WAEC. 


Ga jerin matakai 7 da mutum zai bi kamar haka; 


1. Ziyarci adireshin yanar gizo na shafin WAEC da ake duba sakamakon jarrabawa https://www.waecdirect.org


2. A rubuta lambar WAEC a gurbin da aka samar a shafin 


3. Sai a zabi shekarar da aka rubuta jarrabawa 


4. A cike sunan irin sakamakon da ake son dubawa, wato ''school candidate result'' 


5. Sai a shigar da lambar katin jarrabawa 


6. A shigar da muhimman lambobin katin jarrabawa (PIN) 


7. Sai mutum ya latsa makulin 'aike' (Submit) domin ganin sakamakon jarrabawarsa na WAEC din 2020 


A baya Legit.ng Hausa ta wallafa cewa hukumar WAEC ta saki sakamakon jarabawar daliban da suka kammala babbar makarantar sakandare a wannan shekarar. Shugaban hukumar reshen Najeriya, Patrick Areeghan ya sanar da hakan a ranar Litinin a garin Legas, Premium Times ta wallafa. 


Kamar yadda yace, dalibai 1,003,668 da ke wakiltar kashi 65.24 na dukkan daliban da suka rubuta jarabawar sun samu sakamako mai kyau a darussa biyar da suka hada da darasin Turanci da Lissafi. 


Ya ce dalibai 1,338,348 da suka rubuta jarabawar wanda suke wakiltar kashi 86.99 na jimillar daliban sun samu nasara a a kalla darussa biyar. 


Patrick Areghan ya sanar da cewa, hukumar ta rike sakamako 215,149 na daliban da suka rubuta jarabawar a wannan shekarar. Kamar yadda yace, sakamakon da aka rike na wakilatar kashi 13.98 na jimillar wadanda aka saki. 


Ammaa halin yanzu ana binciken sakamakon wadanda ake zargi da satar jarabawa. Ya ce dalibai 1,549,740 ne suka yi rijistar jarabawar a wannan shekarar, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito. 


SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Duba hanyoyi guda 7 na Yadda za a duba sakamakon jarrabar WAEC ta 2020"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?