
Dan sanda ya bindige wani bawan Allah a otal, ya raunata wani na daban
Monday, 23 November 2020
Comment

Wani dan sanda ya harbi wani saurayi a harabar Otal din Ekiti, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwarsa - Kamar yadda gidan talabijin na Channels suka tabbatar, al'amarin ya faru ne a ranar 21 ga watan Nuwamban 2020
Bayan kashe saurayin, dan sandan ya dauke gawar ya yaddar a asibitin koyarwa na jihar Ekiti, ya tsere Wani dan sanda ya harbi wani saurayi mai suna Olaoye Akintayo, a ranar 21 ga watan Nuwamban 2020, inda take a nan ya rasa ransa.
Saurayin ya raka abokansa otal din Ekiti ne, kamar yadda gidan talabijin din Channels suka tabbatar. Kisan da 'yan sanda suke yi ba tare da kotu ta bayar da izini ba ya kara yawaita ne tun bayan zanga-zangar EndSARS, wanda aka yi don dakatar da cin zarafin da 'yan sanda suke yi.
Kamar yadda abokan mamacin da wasu ganau suka tabbatar, dan sandan ya shigo harabar Otal din cikin wata mota, kirar Hilux, sai dai suka ji karar harbi.
Ba a san abinda ya janyo harbe-harben ba, wanda yayi sanadiyyar raunata wani daban. Dan sandan da abokan aikinsa sun dauki gawar saurayin, inda suka jefar da shi a harabar asibitin koyarwa na jihar Ekiti, daga nan suka ajiye motar a harabar asibitin, suka tsere.
Jami'in hulda da jama'an jihar, Sunday Abutu, ya tabbatar wa da gidan talabijin din Channels cewa an damki dan sandan, duk da dai har yanzu ba a riga an gano dalilin harbin ba.
SOURCE: LEGIT
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Dan sanda ya bindige wani bawan Allah a otal, ya raunata wani na daban"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?