
Dan Najeriya ya lashe zaben kujerar majalisar wakilai a Amurka
Dan Najeriya Oye Owolewa ya zama dan majalisa mai wakiltar Columbia a kasar Amurka bayan ya lashe zabe a karkashin jam’iyyar Democrat - Oye dai ya sami kaso 82.65 cikin 100 wanda ya kai kuri’u 135,234 inda ya kayar da abokan hamayyarsa
Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki ya taya shi murnar wannan nasara da yayi Wani haifaffen dan Najeriya a karkashin jam’iyyar Democrat, Oye Owolewa, ya lashe zaben kujerar dan majalisa mai wakiltan gundumar Columbia a kasar Amurka.
Hakan na kunshe ne a cikin wani wallafa da shafin ABC 7 News tayi a safiyar ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamba. Bisa ga sakamakon zaben, Oye sami kaso 82.65 cikin 100 wanda ya kai kuri’u 135,234 inda ya kayar da abokan karawarsa Joyce Robinson-Paul wanda ya sami kuri’u 15,541, da kuma Sohaer Syed wanda ya samu kuri’u 12,846.
Oye Owolewa mai shekaru 30, ya fito ne daga yankin Omu-Aran da ke jihar Kwara, jaridar Daily Trust ta ruwaito. Owolewa ya kasance daya daga cikin yan Najeriya tara da ke takara a zaben Amurka. Ya kammala karatun digirin digir-gir dinsa a fannin Kimiyyar
Harhada Magunguna daga Jami’ar Norteastern da ke birnin Boston a kasar ta Amurka. Tuni dai ’yan Najeriya da dama suka fara mika sakon fatan alheri da taya murna ga Mista Oye, ciki har da tsohon gwamnan jihar Kwara kuma tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Laraba, Saraki ya ce: "Ina taya Oye Owolewa (@AdeoyeOwolewa) murna, kan zabarsa da aka yi a matsayin dan majalisar wakilai na gudunmar Columbia. Nasararsa wata ’yar manuniya ce kan cewa matasan Najeriya za su iya cimma manyan burikansu a rayuwa."
I congratulate Oye Owolewa (@AdeoyeOwolewa), on his election as a shadow U.S. Representative for the District of Columbia. His convincing victory at the polls is a great testament to the ‘can do’ spirit of all Nigeria’s young people. https://t.co/PpLnmjJ6Tk
— Dr. Abubakar Bukola Saraki (@bukolasaraki) November 4, 2020
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "Dan Najeriya ya lashe zaben kujerar majalisar wakilai a Amurka "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?