
Dan baiwa: Kamfanin motoci na sake kera motar da wani matashin yaro dan shekara 18 ya kera
Koda dai ba a gama tabbatarwa ba, an yarda cewa kamfanin kera motoci ta Kantanka na kera sabuwar ne da hadin gwiwar matashin Kamfanin kera motoci ta Kantanka karkashin jagorancin Shugaban kamfanonin Kantanka Group, ta kera wata sabuwar mota mai suna Kantanka Akofena.
A wani wallafa da Legit.ng ta gano a shafin Twitter na shugaban, ya wallafa wani hoto na motar wacce har yanzu ake kan aiki a kanta a kamfanin. Motar ta Akofena, kamar yadda aka nuno a hoton, tana dauke da suffa iri guda da tsarin motar da Kelvin Odartey, matashi dan shekaru 18 da ke karamar makarantar sakandare ya kera.
Kalli wallafar a kasa:
Kantanka #Akofena pic.twitter.com/yp8FJukQ6R
— Kwadwo Safo Jnr (@kwadwosafo_Jnr) November 17, 2020
A tuna cewa wani bidiyo na matashi dan shekaru 18 da ya kammala karamar makarantar sakandare ya yi fice a soshiyal midiya a yan makonnin da suka gabata, bayan ya kera wata mota da kayan gwangwan.
Bayan nan ne matashin ya samu gurbin karatu kyauta daga wajen Kwadwo Safo Junior. An tattaro cewa matashin wanda ya birge mutane da dama a shafin soshiyal midiya ya tuka motar da ya kera da hannunsa zuwa cibiyar rubuta jarrabawa domin rubuta jarrabawarsa ta karshe.
Koda dai ba a tabbatar ba, an yarda cewa kamfanin kera motoci ta Kantanka na kera sabuwar motar da hadin gwiwar matashin ne.
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "Dan baiwa: Kamfanin motoci na sake kera motar da wani matashin yaro dan shekara 18 ya kera "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?