--
Da gangan na dinga lalata da kanwar matata don in bata mata rai - Magidanci

Da gangan na dinga lalata da kanwar matata don in bata mata rai - Magidanci


Abinda namiji zai yi ya azabtar da matarsa shine yayi tarayya da 'yar uwarta, don na gwada kuma na tabbatar, inji wani mutum - Mutumin mai suna Maduakor Wiseman Jesus, ya yi tunkaho da karshen cutarwar da yayi wa matarsa har ta tafi ta bar shi da jariri 


Ya shawarci maza cewa idan suna so su yi maganin matansu su yi tarayya da 'yan uwansu, ba za su taba yafewa ba har abada Babu abinda yafi yi wa kowacce mace radadi kamar mijinta ya ha'inceta da 'yar uwarta. 


Wani mutum dan Najeriya mai yara 2, mai suna Maduakor Wiseman Jesus ya ce babbar hanyar da namiji zai yi maganin matarsa idan ta bata masa rai shine yayi tarayya da 'yar uwarta. 


A cewarsa, "Idan matarka ta bata maka rai, kuma kana so ka azabtar da ita, ka fara tarayya da 'yar uwarta ta jini, kuma ka tabbatar ta gano, yafi musu radadi fiye da kayi tarayya da wasu a waje". 


Kamar yadda ya rubuta, matarsa ta bar shi da jaririya bayan ta gano yana tarayya da kanwar ta. "Ba na wallafa abinda na san ba ya aiki. Za ta karasa rayuwarta cikin bala'i da tashin hankali. Na kasance ina ha'intar mata ta da kanwarta. 


"Bayan ta gano, sai na bata hakuri tun da na gano wannan hanyar. Ta tafi ta barni da jaririya. Bata sake waiwayata ba, muka rabu. "Ta haka na gano cewa wannan al'amarin ya fi komai azabtar da su. Ina so in sanar da ku wannan dabarar ne, a matsayina na mutum mai wayau" a cewarsa. 


SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Da gangan na dinga lalata da kanwar matata don in bata mata rai - Magidanci "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?