--
Da duminsa: 'Yan Boko Haram sun yi wa manoman shinkafa 44 yankan rago a Borno

Da duminsa: 'Yan Boko Haram sun yi wa manoman shinkafa 44 yankan rago a Borno


Yan Boko Haram sun kashe manoma 44 a garin Zabarmari da ke Jihar Borno - Rahotanni sun ce 'yan ta'addan sun afkawa manoman yayin da suke aiki a gonakinsu ne 


Dan majalisar tarayya da kuma majiyoyi da dama daga garin sun tabbatar da afkuwar lamarin Wasu da ake zargin mayakan kungiyar ta'addanci ta Boko Haram ne sun kashe manoman shinkafa a kalla guda 44 a yayin da suke gurbe amfanin gonarsu a cewar dan majalisa da wasu majiyoyi. 


Majiyoyi daga Zabarmari, wani gari a Borno da ya yi fice wurin noman shinkafa sun sanar da Premium Times cewa an kai wa manoman hari ne a lokacin da suke aiki a gonakinsu da ke Garin Kwashebe. 


An kai wa manoman hari ne a ranar Asabar a yayinda mutanen garin ke zaben shugabanin kananan hukumomi, karo na farko a cikin shekaru 13. 



Majiyoyi sun ce "yan ta'adddan sun tattara manoman cikin kankanin lokaci an musu yankan rago." Hassan Zabarmari, tsohon shugaban kungiyar manoman shinkafa a Jihar Borno, ya tabbatarwa majiyar Legit.ng afkuwar lamarin ta hirar wayar tarho. 



"Abin bakin cikin ya faru misalin karfe 11 na safen yau," ya ce a ranar Asabar. "An kai wa manoman hari a gonakin shinkafarsu da ke Garin-Kwashebe a cewar rahotannin da muka samu da rana, an kashe kimanin 40 cikinsu." 


Dan majalisa wakilai na tarayya, Ahmed Satomi, wanda ke wakiltan mazabar Jere shima ya tabbatar da afkuwar lamarin a hirar da ya yi da Premium Times. "Abinda ya da faru yau a gonakin shinkafa na Zabarmari abin bakin ciki ne matuka," a cewarsa. 



"An yi wa manoma da masunta kisar gilla. Kawo yanzu mun samu gawarwarki 44 daga gonakin kuma muna shirin musu jana'iza gobe idan Allah ya kai mu." Dan majalisar ya ce an kaiwa manoman harin ne "saboda a ranar Juma'a sun kama wani dan Boko Haram da ya dade yana adabarsu." 



Kakakin rundunar 'yan sandan Jihar Borno, Edet Okon, bai amsa wayarsa ba da aka kira shi a daren ranar Asabar. Bai kuma amsa sakon WhatsApp da aka aike masa ba


SOURCE: LEGIT

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Da duminsa: 'Yan Boko Haram sun yi wa manoman shinkafa 44 yankan rago a Borno "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?