
Da duminsa: Munirat Abdulsalam ta bar Musulunci, ta bayyana dalilinta
Fitacciyar malamar mata mai magana a kan auratayya a kafafen sada zumuntar zamani, ta bar addinin Musulunci - Ta sanar da hakan a wata wallafar da tayi a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Facebook a ranar Lahadi
Kamar yadda tace, bata so a sake alakanta ta da addinin Islama duk da shekaru biyu da tayi a cikinsa Munirat Abdulsalam, fitacciyar malamar mata kuma mai tattaunawa a kan harkar auratayya, ta bar addinin Musulunci.
Idan za mu tuna, kusan shekaru biyu da suka gabata ne ta dawo addinin Islama inda aka lakana mata kalmar shahada tare da nuna mata wankan komawa addinin Musulunci a babban masallacin kasa da ke Abuja.
Kwatsam, a jiya Lahadi sai ga wata wallafarta a shafinta na Facebook wacce ta janyo cece-kuce. Kamar yadda ta wallafa, "Daga yau, bana so a sake danganta ni da Musulunci, domin a cikin shekaru biyu da suka gabata bayan na karba addinin, ban tsinci komai ba da ya wuce barazanar kashe ni, zagi da kirana sunaye.
"Ba su taba daukata a matsayin daya daga cikinsu ba balle su nuna min wata kauna a matsayina na marainiya kuma yarinya mace da ta tashi a wannan al'ummar. "Abu daya nake bukata shine a karrama ni kuma a karbeni, wanda na gaji har yanzu ban samu ba. Za ku iya kasheni a yanzu idan kun ga dama, amma na gaji da wannan tsangwamar."
From today I do not wish to be affiliated with islam, for the past 2 years that I've reaccept islam I got nothing apart...
Posted by Muneerat Abdulsalam on Sunday, 8 November 2020
SOURCE: LEGIT
0 Response to "Da duminsa: Munirat Abdulsalam ta bar Musulunci, ta bayyana dalilinta "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?