--
Da duminsa: Kannywood ta kori Rahama Sadau, ta bukaci sauran jarumai da su yanke alaka da ita

Da duminsa: Kannywood ta kori Rahama Sadau, ta bukaci sauran jarumai da su yanke alaka da ita


An kori jarumar Rahama Sadau daga masana'antar fina-finan hausa da aka fi sani da Kannywood - Korar na zuwa ne sakamakon batanci da ga manzon Allah da wasu hotuna da jarumar ta fitar suka janyo a dandalin sada zumunta 


Kungiyar masu shirya fina-finan Hausa, MOPPAN cikin sanarwar da ta fitar ta ce ba za ta amince da abinda jarumar tayi ba kuma ta yi kira a kaurace mata Kungiyar masu shirya fina-finan Hausa ta Najeriya, MOPPAN ta sake korar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, sakamakon wallafa zafafan hotunan ta a dandalin sada zumunta 


da hakan ya janyo batanci ga Annabi Muhammadu (SAW). Idan za a iya tunawa cikin 'yan kwanakin nan hotunan da jarumar ta fitar sun bazu sosai a dandalin sada zumunta tare da janyo cece-kuce inda wasu ke ganin shigar da ta yi a hotunan bai dace ba. 


Da ya ke fitar da sanarwar a ranar Talata, mai magana da yawun kungiyar MOPPAN na kasa, Al Amin Ciroma ya bayyana abinda jarumar ta yi a matsayin 'abin tir da ba za a amince da shi ba.' Kungiyar ta tunatar cewa a Oktoban 2016 ta taba korar jarumar saboda saba dokokin ta inda ta 'rungumi wani mawaki Classic a bidiyon wani wakarsa.' 


Kungiyar ta masu fina-finai na Arewa ta kuma yi kira ga sauran kungiyoyi da ke harka da Kannywood su tabbatar sun yi biyaya ga dokar. Wani sashi na sanarwar ya ce, "Kungiyar masu shirya fina-finan Hausa ta Najeriya, MOPPAN, kungiyar gamayyar masu fina-finai a arewa (da aka fi sani da Kannywood) ta matukar damuwa kan sabbin hotunan da jaruma Rahama Sadau ta wallafa a shafukan sada zumunta.



"Hotunan da tuni sun bazu a dandalin sada zumunta da dama. "Hotunan sun janyo maganganu har ta kai ga cewa ana batanci ga manzon tsira - Annabi Muhammad (SAW) a Twitter da wasu dandalin sada zumunta. Wannan a cewar sakataren MOPPAN na kasa abin tir ne da ba za mu amince da shi ba." 


Hakan yasa MOPPAN ta sake korar Rahama Sadau kamar yadda ta taba yi a Oktoban 2016 kana ta bukaci sauran masu harka masana'antar su kaurace yin aiki da ita. 


SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

 

Related Posts

0 Response to "Da duminsa: Kannywood ta kori Rahama Sadau, ta bukaci sauran jarumai da su yanke alaka da ita "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?