--
Da duminsa: Jam'iyyar PDP zata sake rasa gwamna ɗaya, in ji Wike

Da duminsa: Jam'iyyar PDP zata sake rasa gwamna ɗaya, in ji Wike


Nyesome Wike, gwamnan Jihar Rivers ya gargadi jam'iyyar cewa wani daga cikin gwamnan ta zai sake barin jam'iyyar - Amma Wike bai bayyana sunan gwamnan da ya ke nufi ba kuma bai sanar da takamaiman ranar da gwamnan zai fita ba 


Wike ya yi ikirarin cewa dama wasu gwamnonin na PDP suna harka da APC cikin dare amma da rana su rika nuna cewa sun 'yan PDP ne Gwamnan Jihar Rivers Nyesome Wike ya ce wani gwamnan guda daya daga jam'iyyar PDP zai sake ficewa daga jam'iyyar ya koma wata kamar yadda Channels Television ta ruwaito. 


"Ina fada maka, akwai wani gwamnan PDP guda daya da zai sake barin jam'iyyar," a cewar Wike yayin hirar da aka yi da shi a shirin Politics Today. Amma Gwamna Wike bai fadi sunan gwamnan ba da kuma ranar da zai fice daga jam'iyyar ta PDP. 


Kamar yadda Umahi ya yi, yana tsammanin shima wannan gwamnan sai bijiro da wani dalili a yayin da i zai fice daga jam'iyyar. "Maganar dama wadannan gwamnoni ne da sun dade suna yi wa jam'iyya zagon kasa. 


Suna 'soyayayya' da APC cikin dare amma da rana su fito su ce sun 'yan PDP ne," in ji shi. Batun yi wa jam'iyya zagon kasa ya dade yana damun Wike amma kamar jam'iyyar ta PDP bata dauki batun da muhimmanci ba kamar yadda ya kamata. 


"Matsala ta da jam'iyyar mu shine idan ka fadi gaskiya sai a taso maka, na sha taso da wannan maganar sau da yawa." Ficewar Umahi daga jam'iyyar ta PDP ya janyo cece-kuce kuma ta rage adadin jihohin da jam'iyyar PDP ke da su a yankin Kudu maso Gabas. Yanzu APC ita ke da jihohin Imo, Ebonyi yayin da APGA ke da Anambra. 


SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Da duminsa: Jam'iyyar PDP zata sake rasa gwamna ɗaya, in ji Wike "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?