
Da duminsa: Jakadan Najeriya a kasar Jordan ya kwanta dama
Sunday, 1 November 2020
Comment
Jakadan Najeriya a kasar Jordan, Haruna Ungogo ya rasu a ranar Lahadi - Ya rasu ne bayan kwantar da shi asibitin Garki da ke Abuja da kwana biyar - Majiya daga iyalinsa ta ce za a yi jana'izarsa a ranar Litinin a Kano Haruna Ungogo, jakadan Najeriya a kasar Jordan,
masarautar Hashmite da ke Jordan da Iraq, inda ya rasu yana da shekaru 75 da haihuwa. Daily Nigerain sun tattaro bayanai a kan mutuwarsa a ranar Lahadi da safe a asibitin Garki da ke Abuja, bayan kwantar da shi da aka yi da kwana biyar.
Majiya daga iyalansa ta ce za a yi jana'izarsa a Kano ranar Litinin. Yayi aiki da gwamnatin Kano a matsayin sakataren gwamnati, daga baya kuma ya zama shugaban Folitakanik da ke jihar Kano.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabesa a matsayin jakada a shekarar 2016.
SOURCE: LEGIT.NG
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Da duminsa: Jakadan Najeriya a kasar Jordan ya kwanta dama "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?