
Da duminsa: Dogarin kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bindige mai siyar da jarida ba gaira, ba dalili
Kuma dai, wani dan sanda ya bindige dan kasuwa cikin kure - Kakakin majalisar wakilai, wanda dogarinsa ya aikata kisan ya bayyana alhininsa Wani jami'in dan sanda dake gadin kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bindige wani mai sayar da jarida a birnin tarayya, Abuja ranar Alhamis.
Kakakin majalisar da kansa ya tabbatar da hakan a shafinsa na Tuwita. Ya bayyana cewa da yamma bayan tashi daga Ofis, ya tsaya hira da wasu masu sayar da jarida a harabar majalisar dokoki yayinda wasu batagari suka tare motarsa.
Kakakin ya ce hadimansa sukayi harbi sama domin koran batagarin, amma daga baya ya samu labarin cewa harsashi ya samu wani. Gbajabiamila ya ce wannan abin ya tayar masa da hankali. "Wani abin takaici ya faru.
Da yammacin nan yayinda nike fita daga majalisar dokoki, na tsaya kamar yadda na saba domin gaisawa da masu sayar da jaridun dake kwana. Da yawa cikinsu sun san ni tun lokacin da na dawo Abuja kuma abokai na ne," yace "
Amma, yayinda dogarai na suka karaso wasu matasa sun tare motarmu kuma hakan ya sa daya daga cikin dogaran yayi harbi sama domin tarwatsa su." "Awanni bayan haka, bayan mun isa idan muka je, na samu labarin cewa harsashi ya samu wani, sabanin bayanin da na samu a baya cewa sama kawai sukayi harbi."
Tsohon dan takaran shugaban kasa, Omoyele Sowore, ya bayyana sunan mai jaridan da aka kashe matsayin Ifeanyichukwu Elechi.
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "Da duminsa: Dogarin kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bindige mai siyar da jarida ba gaira, ba dalili "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?