
Buhari ya amince da kashe N62.7bn domin gina titin Kano-Dawakin Tofa-Gwarzo-Dariyo
Shugaba Buhari ya jagorancin zaman majalisar zartaswa ranar Laraba - Har yanzu, ministocin Buhari marasa kudirin gabatarwa na musharaka a ganawar ta yanar gizo
An amince da muhimman ayyuka biyu a zaman yau Majalisar zartaswan tarayya FEC karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta amince da amfani da kudi N62.7bn domin ginin titin Kano
Dawakin Tofa-Gwarzo-Dariyo a jihar Kano. Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya sanar da hakan ranar Laraba yayin hira ga manema labarai, inda yake za'a kammala aikin cikin watanni 24 kacal, Daily Trust ta ruwaito.
Hakazalika, FEC ta amince da amfani da N470,263,037 wajen sayan kayayyakin horo a tashar jirgin saman Murtala Mohammed dake Legas.
A bangare guda, jami'in binciken hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, Adariko Micheal, a ranar Laraba ya bayyana abinda akayi da kudin makaman da ake zargin Dasuki da karkatarwa.
Micheal ya ce an kashe N2.2 billion kan addu'ar kashe karshen Boko Haram a Najeriya da Sauidyya. Jami'in ya bayyana hakan ne yayinda yake magana a matsayin shaida a kotu a shari'ar Sambo Dasuki,
tsohon mai baiwa kasa shawara lokacin gwamnatin Jonathan wanda ake zargi da wawushe kudin makamai dala bilyan biyu.
SOURCE: Legit
0 Response to "Buhari ya amince da kashe N62.7bn domin gina titin Kano-Dawakin Tofa-Gwarzo-Dariyo "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?