
Buhari da sauran shugabannin kasashen duniya sun taya Biden murna
Shugaba Muhammadu Buhari da takwarorinsa na kasashen duniya sun taya Joe Biden murnar lashe zabe
Bayan taya murnar, Buhari ya yi fatar Mista Biden zai kyautata alaka da Najeriya da Afirka musamman a bangarori kamar tattalin arziki, tsaro, siyasa da diflomasiyya
Sauran kashashen da suka taya Biden murna sun hada ba Burtaniya, Greece, Ireland, Canada, Jamus, Faransa,
Beligium da sauransu Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaban Amurka Joe Biden murna kan zabensa a matsayin sabon shugaban Amurka.
Buhari a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Twitter a daren ranar Asabar ya yi kira ga Mista Biden ya "ya kara kusantar kasashen Afirka bisa girmama juna da batutuwan da juna za su amfana."
Da ya ke magana kan alakar kasa da kasa, ya bukaci zababben shugaban kasar "ya yi amfani da kwarewarsa wurin magance mummunan siyasar son kai na kawai a siyasar duniya da ya janyo rarrabuwar kawuna."
"Nasarar ka darasi ne da ke tunatar da mu cewa demokradiyya ce tsarin gwamnati mafi kyau don tana bawa mutane damar canja gwamnati cikin lumana," in ji Buhari.
Congratulations to US President-Elect Joe Biden on his election at a time of uncertainty and fear in world affairs. His election is a reminder that democracy is the best form of government because it offers the people the opportunity to change their government by peaceful means. pic.twitter.com/srv3PP6LBz
— Muhammadu Buhari (@MBuhari) November 7, 2020
Har wa yau, Buhari ya ce yana fatan samun ganin hadin kai tsakanin Najeriya da Amurka musamman bangarorin tattalin arziki, diflomasiyya, siyasa da tsaro.
Sauran shugabanni kasashen duniya suma sun bi sahun Buhari wurin mika sakon taya murna ga Mista Biden.
Cikin wadanda suka mika sakon taya murnar akwai shugabannin kasashen Ireland, Canada, Burtaniyya, Faransa da Jamus. Sauran su ne Greece, Belgium da Tarayyar kasashen Turai.
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "Buhari da sauran shugabannin kasashen duniya sun taya Biden murna "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?