
Budurwa ta bayyana barnar da Gtayi wa saurayinta bayan ta gano zai auri wata
Wata budurwa ta sanar da matakin da ta dauka bayan ta gano saurayinta zai auri wata daban
Ta ce sai da ta tabbatar da kayan da zai sa ranar daurin auren, sai ta lalata su - Ta yi amfani da almakashi ta yayyanka kayan,
sannan tayi fatan ba zai gano ba sai ranar bikin Wata mata ta bayar da labarin matakin da ta dauka bayan ta gane saurayinta zai auri wata daban.
Matar ta yi amfani da shafinta na Twitter inda ta fadi abinda ta yi wa saurayinta bayan jin za a daura masa aure da wata.
Ta sanar da labarin ne bayan OAP Toolz ya tambayi mutane a kan matakin da suka dauka bayan an yaudaresu. Matar ta amsa da:
"Bayan na gano cewa zai yi aure, na samu almakashi ba yayyanka kayan da zaisa a ranar auren, hakan ya faru jiya ne."
Ta kara da cewa, sai da ta yi fatan bai gane ta lalata rigar ba har sai yayi lattin siyan wata rigar, kenan ranar auren, yadda ba zai iya siyan wata ba.
SOURCE: Legit
0 Response to "Budurwa ta bayyana barnar da Gtayi wa saurayinta bayan ta gano zai auri wata "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?