
Binciken gida-gida: Shehu Sani ya yi martani mai zafi ga gwamnati
A wurin gwamnoni, indomie ta zama gwal, yayin da rayuwar mutane ta zama azurfa, cewar tsohon sanata Shehu Sani - Ya wallafa hakan ne a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani, inda ya nuna yadda gwamnati take kaskantar da mutane
'Yan Najeriya da dama sun yi na'am da wallafarsa, inda suka yi ta tsokaci iri-iri da ke nuna amincewarsu da wannan maganar Tsohon sanata Shehu Sani, ya ce wasu gwamnonin sun fi daraja indomie fiye da rayuwar jama'a.
Ya fadi hakan ne a matsayin martani a kan bin gida-gida da gwamnoni suka umarci jami'an tsaro don kwato kayan abincin da mutane suka sata daga ma'adanar gwamnati. Idan ba'a manta ba, sakamakon zanga-zangar EndSARS da ta koma rikici, matasa sun balle ma'adanar gwamnati suka yi ta satar kayan abinci.
Kamar yadda wasu bidiyoyi suka bayyana, yawancin matasan, kayan abinci suka yi ta kwasa cikin kwanaki 13. Bayan faruwar lamarin ne gwamnoni suka umarci hukuma da su bi gida-gida wurin binciko kayan.
Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa, ya tsoratar da 'yan jiharsa, inda yace zai sa a rushe gidan duk wanda aka kama da kayan tallafin. A wata wallafa da Shehu Sani yayi a ranar Asabar, yace: "A wurin gwamnoni, indomie ta zama zinari, yayin da rayuwar mutane ta zama azurfa."
Bayan wannan wallafar, mutane da dama sun yi ta tsokaci, suna nuna amincewarsu da maganar sanatan. Ga wasu daga cikin tsokacin: Wani Gbemi Nath Olorungbon cewa yayi, "Mafi yawan 'yan siyasanmu basu san darajar rayuwar mutane ba sai lokacin zabe."
TheGreatKhalid ya ce, "Gwamnatinmu za ta iya zuwa gida gida don nemo kayan tallafi amma ba za ta iya bin kananun hukumomi ba don raba kayan tallafin."
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "Binciken gida-gida: Shehu Sani ya yi martani mai zafi ga gwamnati "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?