--
Bidiyon yadda jama'a suka yi wa wani mutum dukan mutuwa a kan satar dan kamfai

Bidiyon yadda jama'a suka yi wa wani mutum dukan mutuwa a kan satar dan kamfai

 Wani bidiyo ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta, wanda aka kama wani barawon da dan kamfai - Barawon ya lallaba cikin wani dakin mata, tare da mai raka shi, wanda shi yake nuna masa hanya 


Mutumin kuwa ya sha duka, inda ya rasa inda zai sa kansa, hakuri kawai yake bayarwa An kama wani barawon dan kamfan mata, ana tsakiyar fargabar satar kamfai a Najeriya, inda ake zargin tsafi ake yi da shi. 


Mutumin ya shiga wani gidan mata, tare da mai raka sa har cikin gidan, The Nation ta wallafa. Saurayin ya bude wani akwati, yana tsakiyar kwasar wandunan, sai mai su ta damke shi. 


Ta rasa abinda za ta yi masa, kawai sai barawon mai karfin hali ya fara bata hakuri. Take a nan aka gayyaci maza suka fara dukanshi, inda ya sha bakar wahala a hannunsu. 

SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Bidiyon yadda jama'a suka yi wa wani mutum dukan mutuwa a kan satar dan kamfai"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?