--
Bidiyon wata mata da ake zargi da satar mazakutar wani mutum a Aba

Bidiyon wata mata da ake zargi da satar mazakutar wani mutum a Aba


Wasu mutane a garin Aba, Jihar Abia sun zargi wata mata da satar mazakutar wani mutum - Sunyi ikirarin cewa ta roki mutumin ya taimaka mata da kudi kwatsam sai ta sace masa mazakuta 


Duk da cewa matar da musanta abinda ake zarginta, sunyi ikirarin ta mayar masa ne bayan anyi barazanar dukan ta Wani abin tashin hankali ya faru a Aba inda mutane suka taru a suka zagaye wata mata suna zarginta da sace wa wani mutum azakarinsa sannan ta mayar masa. 


A wani hoton bidiyo da ya bazu a dandalin sada zumunta, ana iya ganin matar da alamun kumburi a fuskarta da wuyan ta tamkar an mata duka kamar yadda LIB ya ruwaito. 


Mutane sun taru suna zargin ta cewa ta tafi wurin wani mutum ta roki ya taimaka mata da kudi kuma bayan ya bata zai ya ji wani ya girgiza sannan ya nemi mazakutarsa ya rasa a lokacin da ya yi kokarin fitsari. 



Sun yi ikirarin cewa daga baya ta dawo masa da azakarin bayan an taru an kanta anyi barazanar mata duka. Sai dai matar kamar yadda bidiyon ya nuna ta ce ba ta sace masa mazakuta ba balantana ta mayar masa. 



Tana tambayar ta yaya ta mayar masa idan har ta sace. Duk da ta musanta hakan, sun cigaba da kasancewa a kan bakansu na cewa ta sace masa mazakuta sannan ta mayar masa. 


Ana iya ganin mutum da ake ikirarin an sace masa mazakutar sanya da riga mai launin bula tare da mutane suna masa rakiya zai shiga dakin gwajin na likitoci. 



Sun yi bayanin cewa za su tafi dakin gwajin ne domin tabbatar da cewa mazakutar mutumin tana aiki yadda ya dace. A yayin da matar ke musanta satar mazakutar, ana iya jin wata murya daga cikin mutanen da suka taru na barazanar kona ta. 


Ga dai bidiyon a kasa: 



View this post on Instagram

An outrageous scene played out in Aba as a crowd gathered around a woman to accuse her of stealing and returning a man's penis. In a video shared online, the woman is seen with red marks on her face, neck, and chest, like she had been assaulted. A crowd gathers around her, making accusations that she approached a man begging him for money and the moment the man gave her money, he felt a shock then noticed his penis had disappeared when he tried to pee. They claim she later returned the penis after they gathered and threatened her. However, the woman is seen in the video insisting she didn't steal or return any penis. She asked the crowd how exactly she returned the penis if she had stolen it. Despite her denials, they keep insisting she stole and returned the penis. The man whose penis was allegedly stolen is also seen in a sky blue shirt as the crowd walks with them to a lab. They explain in the video that they are going to a lab to test and be sure the man's penis is still functional. As the woman denies the penis theft allegations, a voice in the crowd is heard threatening to set her on fire.

A post shared by Lindaikejiblog (@lindaikejiblogofficial) on



SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Bidiyon wata mata da ake zargi da satar mazakutar wani mutum a Aba "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?