
Kalli Bidiyon soji suna ragargazar 'yan bindiga suna tsaka da taronsu a Kaduna
Dakarun sojin Najeriya na ci gaba da samun manyan nasarori a bangaren tabbatar tsaro - Hedkwatar tsaro ta kasa ta wallafa bidiyon ragargazar da sojin sama suka yi wa 'yan bindiga a Kaduna - Kamar yadda aka gani,
'yan bindigar sun kwaso shanu daruruwa yayin da suke yunkurin barin dajin Kuzo Dakarun sojin saman Najeriya sun yi wa 'yan bindiga ruwan wuta ta jirgin yaki a yankin Kuzo da ke jihar Kaduna. Rundunar karkashin Operation Thunder Strike ta tabbatar da kisan 'yan bindiga masu yawa a wannan samamen da ta kai.
Kamar yadda bidiyon da hedkwatar tsaro ta wallafa a shafinta na Twitter ya bayyana, sojin saman ta jiragen yaki sun tare 'yan bindigar a Kuzo yayin da suke kokarin fitar da shanun sata daga dajin. An ga 'yan bindigan suna yunkurin fitar da daruruwan shanu daga dajin a ranar 7 ga watan Nuwamban 2020.
Kamar yadda Manjo Janar John Enenche ya bayyana, an hango 'yan bindigar ta bangaren gabas maso yammacin dajin sannan sojin suka yi musu ruwan wuta. Hakan yayi sanadin mutuwar 'yan bindigan masu tarin yawa a take
KALLI BIDIYON AQASA:
#pressrelease #DHQUpdate
— DEFENCE HQ NIGERIA (@DefenceInfoNG) November 8, 2020
Air Component Of OPERATION THUNDER STRIKE Neutralizes Several Armed Bandits, Distrupts Their Activities In Kuzo Area, Kaduna Statehttps://t.co/BjbEqhDvP2 pic.twitter.com/GomaxJPO2Q
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "Kalli Bidiyon soji suna ragargazar 'yan bindiga suna tsaka da taronsu a Kaduna "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?