--
Bidiyon Emmanuella tana bayanin yadda ta samu kudin gina wa mahaifiyarta katafaren gida

Bidiyon Emmanuella tana bayanin yadda ta samu kudin gina wa mahaifiyarta katafaren gida


Emmanuella Samuel, yarinyar nan mai bidiyon ban dariya ta shayar da mutane mamaki bayan ta gina wa mahaifiyarta gida - Karamar yarinyar, ta bayyana wa duniya yadda ta samu damar tara makudan kudade duk da tana da kananun shekaru 


Ta ce tana raba kudaden da take samu gida 4, kashi daya ta kai gidan marayu, daya gini, dayan iyayenta sai ta adana dayan kason Yarinyar mai shekaru 10 da haihuwa, ta bai wa mutane mamaki ta yadda ta gina wa mahaifiyarta gida. 


Sai da Emmanuella ta cika gidan da kayan alatu, sannan ta bai wa mahaifiyar kyautar gidan, kuma ta yi mata alkawarin mayar da ita wani katafaren gida. A wata tattauanawa da BBC suka yi da ita, ta ce ta so siya wa mahaifinta mota, sai kawunta Mark, ya tuna mata da alkawarin gidan da tayi wa mahaifiyarta. Mark ya shawarceta da ta fara siyan gidan tukunna. 


Emmanuella ta yi wa manajanta magana, inda tace ya dinga raba kudaden da take samu gida 4. Tace kashi daya za ta dinga kaiwa gidan marayu, daya kuma gini, wani kason kuma na iyayenta sai kason na karshe ta dinga adanawa. 



A cewarta, ta yi kusan shekara 1 tana ginin, tun watan Disamban 2019 ta fara. Tayi matukar farin cikin ganin yadda iyayenta suka shiga matsanancin farinciki, musamman yadda mahaifiyarta tayi ta farinciki. 


Tace mahaifiyarta ta cancanci gidan da yafi haka. Kuma tana nan da burin siya wa mahaifinta mota. Jaridar Legit.ng ta yi hira da uncle Mark, inda yace yarinyar diyar makwabciyarsa ce, ya dauketa ne bayan ya ga yana bukatar karamar yarinya don su dinga bidiyon ban dariya tare. Kuma tun da ya dauketa yake samun nasara. 


SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Bidiyon Emmanuella tana bayanin yadda ta samu kudin gina wa mahaifiyarta katafaren gida "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?