--
Bidiyo: Takaicin soyayya ya sa matashin Likita fashewa da kuka a gaban marasa lafiya

Bidiyo: Takaicin soyayya ya sa matashin Likita fashewa da kuka a gaban marasa lafiya


An gano wani likitan kasar Ghana da ba a bayyana sunansa ba yana ta rusar kuka bayan budurwarsa mai suna Ewurama ta yaudari zuciyar shi - A cikin biyon, an gano marasa lafiya sun yi layi suna jiran shi ya duba su amma matashin likitan ya kasa tausar zuciyarsa a waje daya 


Mabiya shafin soshiyal midiya sun yi martani ga bidiyon wanda tuni yayi fice a yanar gizo An dauki wani likitan kasar Ghana a wani bidiyo da yayi fice, yana ta rusa kuka kamar karamin yaro bayan budurwarsa ta yaudari zuciyarsa. 


Legit.ng ta gano bidiyon mai ban al’ajabi a shafin Instagram din Celebritiesbuzzgh yayinda yake ci gaba da samun tarin sharhi daga mabiya shafin soshiyal midiya. A cewar matashin da ya nadi bidiyon, sunan budurwar da ta yaudari matashin likitan Ewurama. 


Likitan na a bakin aiki ne sannan yana da marasa lafiya da yawa da ke jiran ya duba su amma ya kasa tausar zuciyarsa waje guda domin gudanar da aikin da ke gabansa. Sai dai, abun bakin ciki a bidiyon shine lokacin da ya kai karshe, sai ya fara rera kuka da sauti. 


Kalli cikakken bidiyon a kasa: 





SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

 

Related Posts

0 Response to "Bidiyo: Takaicin soyayya ya sa matashin Likita fashewa da kuka a gaban marasa lafiya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?