--
Bidiyo: Jarumin mutum ya ceto karensa daga bakin Guzan da yaso yin kalaci da shi

Bidiyo: Jarumin mutum ya ceto karensa daga bakin Guzan da yaso yin kalaci da shi



Wani mutum ya nuna bajinta da jarumta domin ceto rayuwar wani karamin karensa da guza ya kusa yin kalaci da shi - Mutumin ya yi allan baku, ya fada cikin tafkin ruwa tare da shake mukamukin Guzan da ya kama karensa 


Sai dai, mutumin ya ce; ba zai kashe Guzan ba saboda ya na rayuwa ne a gurbinsa, shi dai ya yi sa'a ya ceci karensa Wani mutum mamallakin wani kare za'a iya kiransa da "jarumin duniya" bayan yayi tsalle, yayi allon baku cikin ruwa, ya yi faɗa da wani guza da yake shirin hallaka ɗan kwuikwuyonsa. 


Wani bidiyo da ya karaɗe duniya ya nuna yadda mutumin yake faɗa da guza da hannuwansa don ceto ɗan kwuikwuyonsa da guzan ya yi wuf da shi zuwa cikin ruwa a Florida ta kasar Amurka. 


Richard Wilbanks, daga Florida, Amurka, an gano shi a wani bidiyo yayin da ya daka tsalle ya fada cikin wani ruwa mara zurfi yana ta faman faɗa da guzan don ceto ɗan ƙaramin karen nasa. 


A wani bidiyo mai ban mamaki, mutumin ya yi tsallan baɗake cikin kududdufi, ya shake muƙamuƙin guzan, sannan ya janyo shi daga cikin ruwan a yayin da ya ke riƙe da karen nasa mai suna Gunner. 


Yana gurnani cikin fushi, ya take kan guzar ya zare karen nasa daga bakin guzar, abin mamakin kuma shine ya samu ya tsira ba tare da jin wani mummunan ciwo ba. 


Bidiyon, wanda ma'aikatar kula da dabbobin daji ta Florida ta watsa shi, ya ƙare lokacin Richard yana tsaye kyam a cikin ruwan. Da yake bayani akan al-ajabin da ya afku, ya gayawa gidan talabijin na CNN "muna tafiya ta gefen ruwa sai kawai guzan ya yi tsalle daga ruwan kamar an harbo shi. "Ban taɓa tunanin guza zai iya wannan saurin ba. Hanzarinsa yayi yawa." 


"Karen mai suna Gunner yaji ciwo yayin harin, amma abin godiyar shine ya tsallake rijiya da baya," a cewarsa. Richard ya ce bai yi tunanin lafiyarsa ba kwata kwata, ya ce yana ɗaukan karnukansa tamkar "ƴaƴansa" kuma zai iya sallama komai akansu. "Karen ya ji ciwo kaɗan, ni kuma ya ciji hannuna"a cewarsa. 


Richard da matarsa, Louise Wilibanks, yanzu haka suna tafiya da Gunner da tazarar ƙafa goma tsakaninsu da ruwan, kuma sun ce basa son su a hallaka guzan tunda sun ce yana rayuwarsa ne a gurbinsa. 


SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Bidiyo: Jarumin mutum ya ceto karensa daga bakin Guzan da yaso yin kalaci da shi"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?