--
Bayan Dangote, FG ta sake ware wani dan kasuwa a arewa daga dokar rufe iyakoki

Bayan Dangote, FG ta sake ware wani dan kasuwa a arewa daga dokar rufe iyakoki



Tun a cikin shekarar 2019 gwamnatin tarayya ta rufe iyakokinta na kan tudu; ba shiga, ba fita - A cewar gwamnati, ta yi hakan ne domin bunkasa harkokin kasuwanci a cikin gida 


Tun bayan lokacin, babu labarin shige da fice da mafi yawan kayayyakin kasuwanci idan ba ta barauniyar hanya ba Kamfanin siminti na BUA, mallakar hamshakin dan kasuwa, Abdulsamad Isiyaka Rabiu, ya samu sahalewar gwamnatin tarayya domin fitar da siminti zuwa ketare ta iyakar kan tudu, kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.
 

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanin siminti na Dangote ya sanar da cewa ya samu izinin fitar da simiti ta kan iyakokin kan tudu zuwa kasar Nijar da Togo. 


Wata takarda wadda Victor Dimka,Kwanturolan kwastam sashen tilasta doka da aiki ya sawa hannu don turawa mataimakin kwanturola na ƙasa,wadda gidan jaridar TheCable yayi tozali da ita tayi nuni da cewa sahalewar tazo ne daga ofishin mai bada shawarwari kan al'amurran tsaro na ƙasa. 


"An umarce ni da turo wannan wasiƙar mai lamba NSA/227/C 17 ga watan Yuni 2020 daga ofishin mai bada shawarwari kan harkokin tsaro na ƙasa"a rubutun takardar. 


"Motocin zasu fita kuma su dawo ta jan iyakar madakatar Illela a jihar Sakkwato. "Kusa idanu don tabbatar da cewa motar ta ɗauki iya siminti zuwa jamhuriyyar Nijar sannan ta dawo Najeriya ba tare da komai ɗauke cikinta ba."


A watan Oktoba shekarar 2019, Shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya bada umarnin rufe kan iyakokin ƙasar domin kawo karshen safarar makamai,kayan abinci,da muggan ƙwayoyi zuwa cikin ƙasar. 



Rufe kan iyakokin wadda maƙasudinta shine bunƙasa noma da harkokin kasuwanci gami da ƙarfafa tsaro, ta taka muhimmiyar rawa wajen rushewar harkokin kasuwanci a ƙasashe irinsu Togo, Ghana, da Kwaddebuwa waɗanda suka dogara da Najeriya domin kasuwancinsu,


al-ummomi sama da miliyan 200 ke ƙarƙashin waɗannan ƙasashe. Kasuwanci da dama sun samu naƙasu sakamakon rashin samun damar fitar da kayayyakin da suke sarrafawa sanadiyyar rufe kan iyakokin. 


Bayan Joe Biden ya zamanto zakaran da ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Amurka,wani rahoto da jaridar Quartz Africa ta wallafa, ya yi hasashen yadda gwamnatin Biden zata canja alaƙar Amurka da Nahiyar Afirka bakiɗaya. 

SOURCE: Legit

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Bayan Dangote, FG ta sake ware wani dan kasuwa a arewa daga dokar rufe iyakoki"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?