
Bayan caa a kan Rahama Sadau, Mansurah Isah ta yi wa matan Kannywood fallasa
Mansurah Isah ta yi wa 'yan fim tonon silili, har da zargin madigo, inda tace kowa mai zunubi ne kuma Allah ne mai yafiya
Jarumar ta bayyana zargin a shafinta na Instagram, bayan bayyanar hotunan Rahama Sadau wadanda suka janyo cece-kuce
Ta yi wallafar ne bayan jaruman Kannywood sun yi ta bidiyo suna tsinewa Rahama Sadau, da hijabai a jikinsu Tun bayan bayyanar hotunan Rahama Sadau,
wadanda suka kawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani, mutane da dama musamman 'yan fim suka yi ta yin bidiyo suna la'antarta, har da masu hawayen takaici da bakinciki.
Kwatsam sai ga jaruma Mansura Isah ta yi wata wallafa a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Instagram,mai cike da tonon silili, wacce ta harzukar da wasu daga jaruman fim din.
Mansurah Isah ta ce: "Wallahi da ban so yin magana ba, amma kun sa nayi. Wannan shirmen ya isa haka. Na ga wata da ta fito daga Police station kwanan nan tana wa'azi, mtsww.
"Wata da ta wallafa nonuwanta tana rawa a status ita ma tana wa'azi, wata da kowa ya san karya ce ('Yar Madigo) ita ma tana wa'azi.
Kun gani ko, dukkaninmu masu zunubi ne, sannan mun fi tsoron mutane a kan tsoron Allah a zuciyar mu, amma za mu fito kafafen sadarwa muna nuna na Annabi ne.
"Kowacce in za ta yi magana sai ta saka Hijabi, wa ku ka yaudara? Ku je ku duba shafukansu ba saka Hijabi suke ba. Allah na kallonmu duka,
shin duniya ce za ta yi muku hisabi? "Dukkan ku kun samu wata dama ce ta fito da abinda ya ke cikin zuciyarku.
A gurin Allah ne kadai zan nemi yafiya, kuma shi kaɗai zan yi wa kuka a ɓoye ko a fili a lokacin da na san na aikata laifi kuma na san cewa ban yi daidai ba.
"Wannan ya isheni ishara, ALLAH YA NA SON mai neman gafararsa koda sau nawa zai aikata laifi kuma ya nemi tuba. "Ku saka wannan a kanku ku daina damunmu da wani shirmen bidiyon ku na banza".
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "Bayan caa a kan Rahama Sadau, Mansurah Isah ta yi wa matan Kannywood fallasa "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?