
Ba na nadamar komawa jam'iyyar APC: Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi
Daga karshe, gwamnan Ebonyi ya alanta fitarsa daga jam'iyyar PDP zuwa APC - Gwamna Umahi ya bayyana dalilin da ya sa ya yanke shawarar fita daga PDP Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya bayyana cewa ba ya nadamar sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) daga Peoples Democratic Party PDP.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a birnin Abakaliki yayinda yake hira da manema labarai kan cece-kucen da sauya shekarsa ta haifar, rahoton The Nation.
Gwamnan ya ce ya koma APC ne saboda rashin adalcin da jam'iyyar PDP take yiwa yankin kudu masi gabas. Hakazalika ya bayyana cewa bai yi wani yarjejeniya da APC kan baiwa yankin kujerar shugabancin kasa a 2023 ba.
Kungiyar yan kabilar Igbo a gida da waje, Ohanaeze Ndigbo, ta amince da sauya shekar da gwamnan Ebonyi, David Umahi, daga jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP zuwa All Progressives Congress APC.
An ruwaito cewa Umahi ya bayyanawa jagororin uwar jam'iyyar PDP a wata ganawa a Abuja, ranar Talata, cewa yana son fita daga jam'iyyar ne saboda an ki baiwa yankin Igbo kujerar shugabancin kasa a 2023.
Mataimakin Kakakin Ohanaeze, Cif Chuks Ibegbu, ya siffanta sauya shekar Umahi matsayin aikin kwarai. Ibegbu ya bayyana hakan a hirarsa da jaridar Punch a Enugu ranar Laraba. Ya ce PDP za ta yi rashin hallaci idan bata baiwa yankin Igbo kujerar takarar shugaban kasa a 2023 ba.
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "Ba na nadamar komawa jam'iyyar APC: Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?