
An tura tawagar soji na mata zalla zuwa Anambra (hotuna)
An tura rundunar sojoji na musamman zuwa jihar Anambra domin tabbatar da zaman lafiya - Tawagar wadanda suka samu tarba daga gwamnan jihar, Willie Obiano sun kasance mata zalla
Hakan na zuwa ne bayan an yi fama da rikice-rikice a yankuna da dama na kasar sakamakon zanga-zangar EndSARS Rundunar sojojin Najeriya ta tura tawagar mata zalla zuwa jihar Anambra domin aikin kiyaye zaman lafiya.
Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, ya tabbatar da wannan ci gaban a wani wallafa da yayi a shafin Twitter, inda ya kara da cewar an turo rundunar ta musamman domin tabbatar da tsaron mazauna jihar
“A safiyar yau, na tarbi wata tawagar rundunar soji na musamman da aka turo jiharmu domin taimakawa wajen tabbatar da dawowar zaman lafiya da kwanciyar hankali a Anambra.
“A kullu yaumin muna ba tsaron rayuka da dukiyoyin mutanen Anambra muhimmanci sannan mun jajirce don daukar dukkanin matakan da suka kamata don tabbatar da kowani dan Anambra ya samu zaman lafiya. Ya yi rasuwa da aiki ba tare da tsoro ba.”
We have always prioritized the security of lives and properties of ndi Anambra and we are determined to take all necessary steps to make sure that every Onye Anambra enjoys peace. Live and work without any form of fear.
— Chief Willie Obiano (@WillieMObiano) October 30, 2020
A yan makonnin da suka gabata, zanga-zangar EndSARS wanda ya fara cikin lumana, ya zama hargitsi a yankuna daban-daban na kasar yayinda aka yi sace-sace da lalata dukiyoyin gwamnati da na wasu daidaikun mutane.
Gwamnatin jihar Anambra ta takaita zirga-zirga a kokarin da take na hana yaduwar rikici, amma dai yanzu an sassauta dokar kullen, jaridar The Cable ta ruwaito.
A cewar Obiano, “tawagar ta musamman za ta ci gaba daga inda hazikan jami’an sauran hukumomin tsaro suka tsaya wandan kokarinsu ne ya sa jiharmu ta zamo mafi tsaro a Najeriya.”
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "An tura tawagar soji na mata zalla zuwa Anambra (hotuna)"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?