--
An sake zaɓen sabbin 'yan majalisu musulmai a Amurka

An sake zaɓen sabbin 'yan majalisu musulmai a Amurka


Musulmi sun samu karin kujerun majalisu yayin zaben shekarar 2020 a kasar Amurka - Tsaffin 'yan majalisa musulmi na kasar suma duk sunyi nasarar zarcewa kan kujerunsu 


Wasu daga cikin sabbin 'yan majalisun sun hada da Iman Jodeh, Maure Turner da Madinah Wilson-Anton Fitattun 'yan majalisa musulmai na Amurka duk sun ci zabensu a majalisar wakilai na tarayya yayin da wasu sabbi sun kuma yi nasarar lashe zabe a majalisun jihohi. 


Musulmai 'yan kasar Amurka sun fito kwansu da kwarkwata sunyi zabe a cewar shahararren kungiyar kare hakokin musulmi a kasar, Council on American-Islamic Relations (CAIR). Direktan CAIR na kasa Nihad Awad ya ce: 


"Kafafen labarai da 'yan takara sun fahimci karfin da al'ummar musulmi ke da shi ta hanyar amfani da kuri'unsu yayin zabuka da dama a kasar ciki har da zaben shugaban kasa." 


A daren ranar Laraba, 'yan majalisu musulmai guda uku sun lashe zabensu na komawa majalisun wakilai a mazabunsu. Yan majalisun sun hada da Ilhan Omar a mazabar Minnesota, Rachida Tlaib a mazabar Michigan da Andre Carson na mazabar Indiana. 


Dukkansu uku 'yan jam'iyyar Democrat ne. Tlaib da Omar fitattun 'yan majalisa ne tare da Alexandria Ocasio-Cortez da Ayanna Pressley da ake yi wa lakabi da 'The Squad'. 


Yan majalisun sun fita daban da saura 'yan jam'iyyarsu ta Democrats saboda amfani da kujerarsu wurin yaki da tsare-tsaren Shugaba Donald Trump da ba su amince da su ba. 


A majalisar jihar, Iman Jodeh, musulma 'yar asalin kasar Palestin ta lashe zabe a Colorado. A Oklahoma, Maure Turner ta zama 'yar majalisa musulma na farko da ta lashe zabe yayin da Madinah Wilson-Anton ita ma ta zama ta farko a Delaware. 


A Jihar Wisconsin, Samba Baldeh ya lashe zaben dan majalisar jiha yayin da a Florida, Christopher Benjamin ya lashe zabe shima, dukkansu 'yan jam'iyyar Democrats ne.


 A cewar PEW, akwai musulmi miliyan 3.45 a Amurka wadda bai kai kashi daya cikin 100 na kasar ba. Mafi yawacinsu sun fi yawa ne a New York, Michigan, Illinois da California (TRT World). 


SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

Related Posts

0 Response to "An sake zaɓen sabbin 'yan majalisu musulmai a Amurka "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?