--
An kama ɗan shekara 55 da ƙoƙon kan ɗan adam hudu

An kama ɗan shekara 55 da ƙoƙon kan ɗan adam hudu


Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta cafke wani tsoho mai shekara 55 da ake zargi da mallakar sassan dan adam - An shigar da korafi ne a ofishin 'yan sanda a Ago Iyewa inda DPOn yankin ya jagoranci kama mai laifin 


Kwamishinan 'yan sandan jihar Edward Ajogun iya bada umarnin dawo da batun sashen binciken manyan laifuka SCID Rundunar yan sandan jihar Ogun ta kama wani dan shekara 55, Yesiru Salisu da laifin mallakar sassan dan adam da suka hada da kokon kai guda hudu, busassun hannaye biyu da muka muƙi guda uku kamar yadda Channels tv ta ruwaito. 



A wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan jihar Ogun, DSP Abimbola Oyayemi ya fitar, kama wanda ake zargin ya biyo bayan wani rahoto da aka shigar a ofishin yan sanda na Ago Iwoye. 


Mai magana da yawun rundunar ya bayyana cewa, rahotannin sun bayyana cewa an ga wanda ake zargin da jakar da ake zargin kayan sata ne, kuma da aka tambaye shi meye a jakar, sai ya yar da jakar ya gudu jeji.



"Lokacin da muka karbi korafin, DPOn Ago Iwoye, CSP Paul Omiwole ne ya jagoranci jami'an sa zuwa inda abin ya faru, suka kuma bude jakar ta ganin sassa mutane a ciki," a cewar sa. Oyayemi ya ce sun caje jejin da ya gudu kuma sun gano shi. 


"Da aka matsa masa, wanda ake zargin ya bayyana cewa ya samu hako ne a makabartar kiristoci ta Oke Eri," a cewar sa. Kwamishinan ƴan sandan jihar Edward Ajogun ya bada umarnin dawo da batun sashen binciken manyan laifuka don fadada bincike. 


SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "An kama ɗan shekara 55 da ƙoƙon kan ɗan adam hudu "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?