An Dakatar Da Kwamandan Hisbah Kan Karkatar Da Kayan Tallafi
Saturday, 21 November 2020
Comment
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta dakatar da kwamandanta na karamar hukumar Dala, Suyudi Hassan Muhammad.
Kwamandan Hisbah na jihar, Ustaz Ibn Sina ne ya dakatar da Suyudi bisa zargin karkatar da kayan tallafin COVID-19.
Sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Ibrahim Lawal Fagge ya fitar ce an dakatar da Suyudi Hassan ne na tsawon wata daya.
Hakan na zuwa ne bayan ranar Juma’a an tashi baram-baram a zaman neman maslaha da aka yi da wadanda suka yi korafin da wanda ake zargin da karkatar da kayan tallafin da aka ba su su raba wa jama’a.
Hakan na zuwa ne bayan ranar Juma’a an tashi baram-baram a zaman neman maslaha da aka yi da wadanda suka yi korafin da wanda ake zargin da karkatar da kayan tallafin da aka ba su su raba wa jama’a.
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "An Dakatar Da Kwamandan Hisbah Kan Karkatar Da Kayan Tallafi"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?