
Allah mai iko: Miji ya rasu, matar ta bi shi bayan sa'o'i kalilan
Wani abin al'ajabi ya faru a jihar Anambra inda mutuwa ta dauki wasu mata da miji kusan a tare - Mijin, mai suna Israel Akojede ya fara rasuwa, bayan sa'o'i kadan matar mai suna Esther ta bishi
Sun samu shakuwa kwarai, don aurensu yayi shekaru 72, hatta sutura iri daya suke sawa Wani abin al'ajabi ya faru a Abeokuta, jihar Ogun inda Israel Akojede ya rasu babu dadewa sai matarsa Esther ta bishi, Vanguard ta wallafa hakan.
Duk da tsofaffi ne, shekarar aurensu 72. NAN ta ruwaito yadda al'amarin ya faru a wuraren Gbonagun Obantoko da ke Abeokuta, inda aka sanar da mutuwar Akojede da misalin karfe 3 na dare a ranar Juma'a, 30 ga watan Oktoba, ita kuma matar ta rasu bayan awanni kadan da samun labarin mutuwar mijin nata.
Akojede ya rasu yana da shekaru 103 a duniya, yayin da matar tasa take da shekaru 98. Yaronsu na fari, mai suna Joseph Akojede, wanda ya tabbatar da mutuwar tasu yana da shekaru 70 da haihuwa, inda yace al'amarin ya ba wa kowa mamaki duk da kowa yana tunanin hakan ya faru ne saboda tsananin soyayyar da ke tsakaninsu.
A cewarsa, "Mutuwar tazo mana a ba zata amma kuma kowa yayi ta zaton hakan zai faru. Sai dai abinda nake tunani shine tsabar son da suke yi wa junansu yasa suka bar duniya kusan a tare. "Tun ina yaro nake ganinsu tare, babu abinda ya ke rabasu, hatta suturarsu iri daya suke sanya wa, kuma da junansu suke shawara."
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "Allah mai iko: Miji ya rasu, matar ta bi shi bayan sa'o'i kalilan "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?