
Allah ka hanemu da taurin kai, izza da jin babu wanda ya isa ya fada mana mu ji – Ali Nuhu
Sarki mai Kannywood, Ali Nuhu ya yi wasu kalamai masu ratsa zuciya game da zamantakewa ta duniya - Ali ya roki Allah a kan ya nisanta shi daga abunda zai sanya Shi yin fushi da shi - Har ila yau ya gode ma Allah a kan yadda ya rabu da iyayensa lafiya Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta
Kannywood wanda ake kira da Sarki mai sangaya, Ali Nuhu, ya yi wasu zantuka masu ratsa zuciya. A wata wallafa da yayi a shafinsa na Instagram Jarumin ya yi addu’a a kan Allah ya shiryar da shi da sauran al’umma ta yadda ba za su hadu da fushin Sa ba.
Ali ya kuma roki Allah a kan ya raba su da taurin kai, izza da jin babu wanda ya isa ya fada masu magana su ji koda kuwa daga bakin yayan cikinsu ne.
Allah ka hanemu da taurin kai, izza da jin babu wanda ya isa ya fada mana mu ji – Ali Nuhu Hoto: realalinuhu Source: Instagram Jarumin ya kuma yi hamdala a kan yadda ya rabu da iyayensa lafiya, sannan ya roki Allah ya sa ya kuma gama da duniya lafiya tare da zama abun kwantance na gari. Ga yadda ya wallafa a shafin nasa:
“Ya Allah ka sa mu cika da imani, ka sa mu nisanci duk wani abu da zai zama sanadiyyar jawo mana fushinka.Ya Allah kai ke yin yadda ka so da bayinka. Allah ka shirye mu da duk wani wanda yake da niyyar shiryuwa.Ka hanemu taurin kai, izza da jin babu wanda ya isa ya fada mana mu ji.
“Ya Allah ka bamu ikon fahimtar nasiha ko da daga bakin Ya' yan da muka haifa ne balle abokan zama, magabata da abokan sana'a da masoya na gaske albarkacin fiyayyen halitta Muhammad Rasulillah S.A.W. Allah yadda ka raba mu da iyayen mu lafiya, ka sa mu gama da duniya lafiya. Mu zama ababen kwantance na gari.”
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "Allah ka hanemu da taurin kai, izza da jin babu wanda ya isa ya fada mana mu ji – Ali Nuhu "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?