
Ali Ƙwara Azare 'mai kama ɓarayi' ya riga mu gidan gaskiya
Allah ya yi wa fitaccen mai kama 'yan fashi da barayi Ali Kwara rasuwa a ranar Juma'a - Marigayin ya rasu ne a garin Abuja bayan fama da rashin lafiya
Iyalansa sun sanar da cewa za a yi janaizarsa a mahaifarsa ta Azare da ke jihar Bauchi Shaharren mutumin nan ma kama barayi da 'yan fashi a Najeriya Ali Kwara Azare ya rasu a ranar Juma'a 6 ga watan Nuwamban 2020 Ali Kwara ya rasu ne a babban birnin tarayya Abuja bayan ya yi fama da jinya kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
Marigayin ya rasu ya bar matar aure daya da yara hudu da 'yan uwa da dangi da dama. An haife Ali Kwara ne a garin Azare da ke ƙaramar hukumar Katagum a jihar Bauchi. Ya shahara sosai wajen kama barayi da cikin dazuzzuka sannan daga bisani ya ladabtar da su ya kuma koya musu sana'a da su rike kansu da ita.
Danginsa sun bada sanarwar cewa za a gudanar da jana'izarsa a mahaifansa ta Azare.
A wani labarin, kun ji cewa Jami'an Hukumar Kiyayye Hadurra na Kasa, FRSC, za su fara amfani da bindiga don kare kansu daga sharrin wasu masu amfani da tituna a Najeriya.
Akinfolarin Mayowa, shugaban kwamitin FRSC a majalisar wakilai ta kasa ne ya sanar da hakan yayin kare kasafin kudin hukumar na 2021 a ranar Alhamis 5 ga watan Nuwamba a Abuja. Akinfolarin Mayowa ya yi bayanin cewa dokar ta FRSC ACT na 1992 ta bawa jami'an hukumar ikon rike bindiga.
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "Ali Ƙwara Azare 'mai kama ɓarayi' ya riga mu gidan gaskiya "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?