--
Akwai dalili: Budurwa ta rataye kanta a Kano

Akwai dalili: Budurwa ta rataye kanta a Kano


Wata matashiyar budurwa ta rataye kanta a jihar Kano a gidan da take aiki - Sai dai zuwa yanzu ba a san dalilinta na kashe kanta ba domin bata bar wasika da ke bayani kan hakan ba 


Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da afkuwar lamarin inda ta kaddamar da bincike Wani rahoto da muke samu daga jaridar Punch ya nuna cewa wata matashiyar budurwa mai shekaru 16 a duniya mai suna Bahijja Gombe, ta kashe kanta a gidan da take aiki a Zoo Road, jihar Kano. 


Rahoton ya nuna cewa Bahijja, wacce ta kasance yar asalin jihar Gombe ta kashe kanta ne ta hanyar rataya. Sannan bata bar wani jawabi a rubuce ba wanda zai bayyana dalilinta na daukar wannan tsatsauran mataki na kashe kanta. 


Wata majiya ta ce Bahijja, wacce ke aikin goge-gogen gida da kuma kula da masu siyayya a shagon uwargijiyarta, bata zuwa kowani makaranta.


Majiyar ta ce an tsinci gawarta a cikin wani daki a ranar Asabar da misalin karfe 10:00 na dare, inda ta kara da cewa mazauna yankin na daman zargin akwai wata a kasa. Kakakin yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna, ya tabbatar da afkuwar al’amarin, ya bayyana cewa an tsinci gawar matashiyar a rataye a cikin gidan. 


Ya bayyana cewa tuni aka dauke gawarta zuwa wajen ajiye gawarwaki na asibitin murtala sannan kuma cewa rundunar yan sandan ta fara gudanar da bincike a kan al’amarin domin gano musababbin mutuwarta. 


SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Akwai dalili: Budurwa ta rataye kanta a Kano "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?