
A raba ni da shi, gagarumin mashayi ne kuma yana dukana - Matar aure ga kotu
Wata Munirat Obaro, ta roki kotu ta raba aurensu da mijinta Abdullaziz Mohammed - Ta ce mijin nata yana shaye-shaye, yana kuma dukanta har da yunkurin kasheta - Alkalin ya ce bata kawo gamsassun hujjoji ba,
don haka yaki raba auren Wata matar aure mai suna Munirat Obaro, ta roki wata kotu da ke zama a Gwagwalada ta raba aurenta na shekara 17 da mijinta, Abdullaziz Mohammed, wanda ta ke zarginsa da shaye-shaye. Munirat, mai yara 4,
wacce take zaune a Anguwar Shani, ta zargi mijinta da dukanta akai-akai har da yunkurin kasheta. Mohammed ya musanta zargin da take yi masa, inda yace "Matata tayi min kazafi, duk da a shirye nake da na canja duk halayena wadanda bata so."
Alkali mai shari'ar, Adamu Isah, ya ce shaidun da ta gabatar a gaban kotu basu da karfi don haka kotu ta ki amincewa da raba auren. Yace su cigaba da zama a matsayin mata da miji, Daily Trust ta wallafa.
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "A raba ni da shi, gagarumin mashayi ne kuma yana dukana - Matar aure ga kotu "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?