
A cikin sa'o'i 6, budurwa ta tashi daga Legas zuwa Benin kuma ta koma Legas a babur
Wata jarumar 'yar Najeriya, Fehintoluwa, ta yi tafiya daga Legas zuwa Benin a babur, kuma ta koma cikin sa'o'i 6 - Budurwar ta ce bata sanar wa kowa ba, saboda bata so a hanata aiwatar da abinda tayi kudirin aikatawa
Bayan Fehintoluwa ta je ta koma, ta wallafa hotunanta wadanda ta dauka a kan hanyar ta, a shafinta na Twitter Wata budurwa 'yar Najeriya mai suna Fehintoluwa Okegbenle, ta bayyana tafiya mai nisa da tayi a kan babur, a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter. Mutane da dama sun yi ta yaba wa wannan bajintar da tayi.
Ta yi wallafar ne a ranar Asabar, 21 ga watan Nuwamba, Fehintoluwa ta ce ta kama wannan doguwar tafiyar ne, tun daga jihar Legas zuwa Benin. A cewarta, sa'o'i 6 ta dauka a kan babur, daga tashinta har zuwa da komawarta cikin Legas. Idan ba a manta ba, wannan budurwar ta taba zuwa tun daga Legas zuwa Abuja a kan babur, cikin sa'o'i 13.
Ta ce ba ta taba auna karfi da kuzarinta ba kamar na ranar, duk da dai mutane da dama sun yi ta kokarin dakatar da ita, amma ta jajirce. Wannan karon kuwa, bata yi shawara da kowa ba, ta kama hanya ta tafi. A cewar Fehintoluwa, bata taba tafiya mai ban sha'awa da ta kai wannan ba.
Bayan kammala wannan tafiyar ne ta wallafa a shafinta na Twitter, wanda hakan ya janyo fiye da mutane 13,000 suna yaba mata, sannan fiye da mutane 2,000 suka yada wallafar ta ta. Sannan jama'a da dama sun yi ta tsokaci. Wani Chrysmekus cewa yayi:
"Barka, gaskiya kin yi sauri sosai. Ni kaina ina fatan idan na siya nawa babur din zan gwada makamancin hakan. Ina so in kewaye kasar nan, inje Porthacourt zuwa Maiduguri, Maiduguri zuwa Legas, Legas zuwa Taraba. Daga nan sai in koma Abuja. Ba a lokaci guda ba, kila ko sau daya a shekara."
Solo trip from Lagos to Benin and Back to Lagos on 2 wheels.
— Fehintoluwa Okegbenle (@FehinLean) November 21, 2020
It took 6 hours to and fro
This time, I didn’t tell people, bcos I wasn’t ready for the discouragement, just got on my bike and off I went.
The joy of traveling on my bike is amazing.
Where next?#fehintytours pic.twitter.com/mdcEGn7zhr
Wata Mekkah_medina ta ce: "Sak lokacin da nayi amfani da shi a mota, daga Lagos Island zuwa Alagbado, duk cikin jihar Legas, a kan titi daya." Wata Nwaneri_Richard ya ce: "Ina ga zan siya irin wannan babur din, don yanzu haka na kasa tara kudin mota."
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "A cikin sa'o'i 6, budurwa ta tashi daga Legas zuwa Benin kuma ta koma Legas a babur "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?