
Zanga-Zangar #EndSARS Ta Rikide Zuwa Tashin Hankali A Kano
Tuesday, 20 October 2020
Comment
An kashe mutum hudu tare da jikkata wasu da dama a yankin Sabon Gari da ke Karamar Hukumar Fagge ta jihar Kano bayan a yayin da ake ci gaba da zanga-zangar #EndSARS.
A safiyar Talata wasu gungun matasa suka far wa masu zanga-zangar wadanda suka cika wandonsa da iska domin tsira.
Daga bisani zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali, inda matasa da dama daga unguwar Brigade a Karamar Hukumar Nassarawa da ke makwabtaka da yankin Sabon Gari suka farmaki masu zanga-zangar.
Sai dai rahotannin na bayyana cewa bata-gari ne suka yi amfani da zanga-zangar wajen ta da hankalin al’ummar yankin Sabon Gari da kuma wani bangare na unguwar Brigade.
Bata-garin sun farfasa gilasan motoci tare da kona wasu motocin da aka ajiye a bakin hanya.
Har ila yau, bata garin sun fasa babban shagon sayar da kayayyaki na ‘Galaxy Mall’ da ke kan titin Igbo a Sabon Gari, inda suka sace kayyaki da dama.
Sun kuma fasa shagon saida abinci na ‘Chicken Republic’ da ke kan titin Aiport wanda shi ma suka yi barna a cikinsa.
Daga bisani jami’an ‘yan sanda sun kai dauki ga yankin na Sabon Gari domin kwantar da wutar rikicin.
Source: Aminiya Daily Trust
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Zanga-Zangar #EndSARS Ta Rikide Zuwa Tashin Hankali A Kano"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?