
Zaben 2023: Inyamurai sun fara jawo manyan ‘Yan siyasan Yankin Arewa a jiki
Friday, 16 October 2020
Comment

Ezenwafor ya na ganin idan su ka hada-kai da sauran bangarori, to za a dace Wasu daga cikin mutanen yankin Kudu maso gabashin Najeriya, sun fara zama da takwarorinsu na tsakiyar Arewacin kasar nan a kan 2023. Daily Trust ta ce an yi wani zama a ranar Laraba, 14 ga watan Oktoba, 2020, tsakanin mutanen Ibo da ‘yan Arewa a Makurdi, jihar Benuuwai.
‘Yan siyasar da su ke bayan wanan sabon kawance sun bayyana shirinsu a lokacin da su ka zanta da manema labarai ta bakin wani jagoran tafiyar.
Shugaban ‘yan APC a majalisar dokokin jihohin Kudu maso gabashin kasar nan, Cif Afam Ezenwafor, yana cikin manyan wannan kungiyar. Afam Ezenwafor ya bayyana cewa sun zo Arewa ta tsakiya ne domin nema wa yankinsu goyon-bayan sauran bangarorin kasar a zabe mai zuwa.
“Ba za mu iya yi babu Arewa ta tsakiya ba, kuma wannan yanki ya na tsakiyar kasar nan. Abin da ke rike Najeriya shi ne yankin tsakiyar Arewa.” Ezenwafor ya ce samun hadin-kan wannan yanki ne zai sa Kudu maso gabas ta ci zabe a 2023.
Mista Ezenwafor ya fara neman goyon bayan ‘yan siyasar wannan bangare da ya ke ganin sun yi wa Najeriya waigi domin su kai ga ci a zaben 2023. Shugaban wannan tafiya, George Ugwuja, ya ce kungiyarsu ta na dauke da duka ‘yan siyasar da su ke nemi takarar majalisar dokoki a yankin Ibo a 2019.
Kwanan na ne kuma ku ka ji wata kungiya ta magoya bayan Bola Tinubu, ta kaddamar da yakin neman takarar shugaban kasar tsohon gwamnan na Legas. A daidai wannan lokaci kuma ana ganin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, zai yi takarar kujeran shugaban kasa a karkashin PDP a 2023.
Source: Legit.ng
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Zaben 2023: Inyamurai sun fara jawo manyan ‘Yan siyasan Yankin Arewa a jiki"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?