
Yanzun nan: Dole ta sa an garkame Makarantu ganin zanga-zanga ta ki cinyewa
Zanga-zangar #EndSARS da ake yi ta tursasa rufe Makarantu a Oyo - Kafin nan gwamnonin Jihohi sun maka dokar ta-baci a Legas da Edo
Yanzu haka Sanatoci su na zama na musamman a majalisar dattawa Zanga-zangar da ake ta faman yi a bangarorin Najeriya ya yi dalilin da ya sa aka rufe makarantun kasuwa da na gwamnati a fadin jihar Oyo. Wannan zanga-zanga da akasari matasa su ke gudanar wa ya jawo cikas wajen harkar karantarwa a Oyo,
jim kadan da komawa karatu a kasar. Jaridar The Nation ta ce an rufe makarantun boko a jihar duk da cewa gwamnati ba ta fitar da takarda ta na umurtar a dauki wannan mataki ba.
La’akari da yadda aka gaza kawo karshen wannan zanga-zanga bayan fiye da mako guda ya sa iyaye da dalibai su ka kaurace wa makarantu. Makarantun kasuwa sun aika wa iyayen yara takarda a daren ranar Lahadi, su na bada shawarar a guji kawo yara makaranta saboda halin da ake ciki.
Irinsu yankin Apata, New Garage, 110, Omi Adio, Molete, Beere, Ojoo, Moniya, da titin Ibadan a jihar Oyo ba su shiguwa saboda zanga-zangar da ake yi. A daidai wannan lokaci kuma majalisa ta kira taron gaggawa na musamman a ranar Talata.
Ana tunanin cewa Sanatoci sun shiga bayan labule a majalisar ne domin kawo karshen wannan zanga-zanga da ta ci bangarorin kasar daban-dabam. Bude majalisa yau ke da wuya, Ahmad Lawan, ya bukaci ayi zaman gaggawa da karfe 10:55.
A yau aka ji cewa ‘yan zanga-zanga sun jawo aiki ya tsaya cak a Legas da karfi da yaji. Legas da ta saba tatsar kudin bin hanyoyi ta gagara yin hakan a yanzu. Rufe manyan hanyoyi da kofofin shiga garin da aka yi ya sa jihar ta tafka asarar N230m.
Source: Legit
0 Response to "Yanzun nan: Dole ta sa an garkame Makarantu ganin zanga-zanga ta ki cinyewa "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?