
Yanzu-yanzu: An saka dokar hana fita -ba dare, ba rana- a jihar Legas
Bayan kwanaki 12, gwamnatin Legas ta bi sahun Edo wajen sanya dokar ta baci - An kona ofishin yan sanda dake Orile da safiyar Talata a Legas
Gwamnan ya baiwa ma'aikata sa'o'i uku su koma gidajensu zuwa karfe 4 na rana Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa sakamakon zanga-zanga, kashe-kashe da kone-konen dake faruwa a jihar Legas,
gwamnatin jihar ta saka dokar ta baci a dukkan sassan jihar. Gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita, ranar Talata. Ya baiwa mutanen jihar daman komawa gidajen daga yanzu zuwa karfe 4 saboda daga lokacin ba''a son ganin kowa a waje.
"Na zuba ido kan yadda zanga-zangan #EndSARS da aka fara cikin lumana ya zama wani abu daban da ka iya cutar da al'ummarmu, " yace
"An rasa rayuka da sassan jiki yayinda wasu bata gari ke cakuda da masu zanga-zanga domin aika-aika a jihar mu." "A matsayinmu na gwamnati da ta san aikinta kuma ta shirya amsa bukatun #EndSARS, ba zamu zuba ido muna gani ana tayar da tarzoma a jiharmu ba."
"Saboda haka na sanya dokar hana fita na 24hrs a dukkan sassan jihar daga karfe 4 na yau, 20 ga Oktoba, 2020. Ba'a amince a ga kowa ba illa ma'aikata masu muhimmanci."
Mun kawo muku cewa, wasu da ake zargin 'yan daba ne sun kona ofishin 'yan sanda da ke Apapa Iganmu a jihar Legas kamar yadda The Punch ta ruwaito. Lamarin ya faru ne misalin karfe 9.45 na safiya a cewar wani da abin ya faru a idonsa.
Mai magana da yawun karamar hukumar Orile-Iganmu, Ayo Micheal ya ce, "Eh, an kai hari ofishin 'yan sandan.
Source: Legit
0 Response to "Yanzu-yanzu: An saka dokar hana fita -ba dare, ba rana- a jihar Legas "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?