
Yanzu yanzu: Gwamnatin Adamawa ta sanya dokar hana fita ta awanni 24
Sakamakon fasa rumbunan abinci da matasa suka yi a sassan Jihar Adamawa, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya sanya dokar hana fita na sa'o'i 24 - Dokar ta fara aiki daga karfe 3:00 na yau Lahadi, 25 ga watan Oktoba
Gwamnan ya jinjina wa matasan da suka kame kansu a lokacin zanga-zangar EndSARS Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya sanya dokar kulle na sa’o’i 24 a fadin jihar, sakamakon karya doka da oda da aka yi a Yola, babbar birnin jihar Adamawa.
Fintiri ya kaddamar da dokar kullen ne a wani jawabi na musamman a ranar Lahadi, inda yayi gargadin cewa gwamnati ba za ta nade hannu ta ga wasu mutane na tada zaune tsaye ba a jihar.
Gwamnan ya ce dokar kullen zai fara aiki daga karfe 3:00 na ranar Lahadi. Ya kuma ce rashin dakatar da barnar na iya haddasa Asabar rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ya ce: “Ya ku jama’ar kasa yan uwana, ba za mu bari bata gari da wasu miyagu su ci karensu ba babbaka ba alhalin muna fama da matsalolin ta’addanci, garkuwa da mutane, fashin shanu, fashi da makami da rikicin makiyaya da manoma.
“Saboda haka, na kaddamar tare da sanya dokar ta kulle na har sai baba ta gani a fadin jihar, daga karfe 3:00 na ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoba, 2020.”
Ya yi gargadin cewa an haramta zirga-zirgan ababen hawa a lokacin kulle, sai wadanda aka ba umurni, jaridar Daily Trust ta ruwaito. Ya ce lamarin tsaron ya biyo bayan ayyukan da wasu bata gari suka yi na fasa rumbun ajiya mallakar gwamnatin jihar sannan suka sace kayan tallafin korona.
Gwamnan ya jinjinawa matasa a jihar kan kin bari ayi amfani da su wajen aikata ta’asa tunda aka fara zanga-zangar EndSARS a wasu yankunan kasar.
Ya ce yayinda gwamnati ke mutunta yancin al’umma na neman gyara, ta bayyana cewa akwai hanyoyin nuna fafutuka cikin wayewa.
Source: Legit.ng
0 Response to "Yanzu yanzu: Gwamnatin Adamawa ta sanya dokar hana fita ta awanni 24 "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?