--
Yanzu Yanzu: Buratai ya shiga labule da manyan kwamandojin rundunar soji kan zanga-zangar EndSARS

Yanzu Yanzu: Buratai ya shiga labule da manyan kwamandojin rundunar soji kan zanga-zangar EndSARS

 


A yanzu haka manyan shugabannin rundunar sojin Najeriya sun shiga labule - Taron wanda shugaban hafsan soji, Tukur Buratai ke jagoranta zai tattauna ne kan halin da kasar ke ciki a yanzu - Ku tuna cewa kasar na fuskantar matsalar tsaro tun bayan da matasa suka fara zanga-zangar EndSARS a sassa daban


daban na kasar Shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai, manyan janarori da kwamadojin rundunar na cikin ganawa kan barazanar da tsaron kasar ke fuskanta sakamakon zanga-zangar EndSARS. Jim kadan kafin fara taron, wanda ke gudana a dakin taron soji a hedkwatar rundunar tsaro, Buratai ya soki wasu kungiyoyin kasa-da-kasa da ba a bayyana sunansu ba. 


Ya caccaki kungiyoyin ne a kan barazanar da suke yiwa jami’an soji cewa za su haramta masu fita waje bisa zargin take hakkin dan adam, jaridar The Nation ta ruwaito. Ya bayyana cewa taron zai tattauna tsari da halin da tsaro ke ciki a yanzu a kasar. 


A cewarsa: “Wasu miyagu na mana barazana da yunkurin hana mana fita waje, amma bamu damu ba saboda ya zama dole mu ci gaba da kasancewa a kasar domin inganta ta. “Karon farko da na fara fita daga kasar nan, ina da shekaru 50 kuma na kai matsayin Janar, don haka ban damu ba na kare sauran rayuwata a nan.” 


Source: Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Yanzu Yanzu: Buratai ya shiga labule da manyan kwamandojin rundunar soji kan zanga-zangar EndSARS "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?