--
Yan sanda sun kama matar da ake zargi da yanka yaranta a Kano

Yan sanda sun kama matar da ake zargi da yanka yaranta a Kano


Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta tabbatar da kama matar da ake zargi da yi wa ‘ya’yanta biyu yankan rago - Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna ne ya bayyana hakan a yau Lahadi 


Zuwa yanzu dai kwamishinan ‘yan sandan jihar, Habu Sani ya bukaci a mayar da binciken zuwa sashen binciken manyan laifuka Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama matar nan mai shekaru 26, Hauwa Habibu, wacce ake zargi da yi wa ‘ya’yanta biyu yankan rago a Kano. Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna ne ya bayyana hakan a yau Lahadi, 4 ga watan Oktoba a garin Kano,


 jaridar Vanguard ta ruwaito. Ya bayyana cewa a ranar 3 ga watan Oktoba, hukumar yan sanda ta samu labarin cewa wacce ake zargin ta sassara yaranta biyu har lahira da adda. Haruna ya bayyana cewa yaran da abun ya cika da su sune Yusuf Ibrahim mai shekaru 6 da Zahra Ibrahim mai shekaru 3. 


“Da muka samu labarin, mun yi gaggawan tura jami’anmu zuwa wajen sannan suka gano cewa an caccaki yaran ne,” in ji shi. Ya ce daga nan ne aka garzaya da su asibitin kwararru na Murtala Muhammad dake Kano inda likitoci suka tabbatar sun mutu. 


Ya kuma ce matar ta yanki wata kanwarta mai suna Aisha Abdullahi mai shekaru 10 da adda wacce ita kuma aka kai ta Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano dake Kano.


Hakazalika kakakin ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Habu Sani, ya bayar da umarnin a mayar da binciken zuwa sashen binciken manyan laifuka na rundunar domin fadada bincike. A wani labari na daban, mun ji cewa wani abun tashin hankali ya afku a Unguwar Sheka da ke karamar hukumar Kumbotso na jihar Kano. 


Mutanen wannan yanki dai sun tashi da alhini na mutuwar wani dan unguwar mai suna Sagir Muhammad wanda ake zargin wani matashi mai suna Abdullahi Muhammad da kashe shi. 


Source: Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Yan sanda sun kama matar da ake zargi da yanka yaranta a Kano "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?