--
Yan sanda sun damke tsohuwar da ta sayar da jikanta N1.3m saboda uban bai biya sadaki ba

Yan sanda sun damke tsohuwar da ta sayar da jikanta N1.3m saboda uban bai biya sadaki ba


Wata tsohuwa ta shiga hannun jami'an tsaro kan laifin sayar da jikanta a kudi N1.3 million - Tsohuwar mai suna Antonia Amos ta yi ikirarin cewa ta yi hakan ne saboda sirikinta ya ki biyan kudin sadakin 'yarta da ya aura 


Mahaifin yaran ne ya kai kara ofishin yan sanda kuma aka damketa Jami'an yan sanda sun ceto wani jaririn makonni biyu da haihuwa a jihar RIvers bayan uwar mahaifiyarsa ta sayar da shi milyan 1.3. 


Yan sanda sun bayyana cewa tsohuwar mai suna Antonia Amos ta sayar da yaron ne saboda mahaifinsa bai biya kudin sadakin auren mahaifiyar ('yarta) ba, Yabaleft ta ruwaito. A cewar rahoton, an damke Antonia ne bayan mahaifin yaron, Christian Duru, ya kai kara ofishin yan sanda. Kwamishanan yan sandan jihar, Joseph Mukan, 


ya ce Antonia ta kai yan sanda inda ta sayar da jaririn. Da farko ta kai yan sandan karamar hukumar Ukanafun dake Akwa Ibom inda aka damke wata mata mai suna Pauline Umoh.


Sannan ta kaisu Mgbidi a jihar Imo wajen wacce ta sayi jaririn, Juliana Obianwa, inda aka kwato yaron kuma aka damketa. A cewar Mukan, yan sanda na kokarin damke sauran mutane dake da hannu cikin wannan aika-aikan. 


Source: Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Yan sanda sun damke tsohuwar da ta sayar da jikanta N1.3m saboda uban bai biya sadaki ba "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?