
'Yan daba sun mamaye fadar Sarkin Legas, sun kwace sandar ikonsa
Wasu matasa da ake kyautata zaton 'yan daba ne sun kai hari fadar Sarkin Legas da ke Igi Idugaran - Matasan sun yi barna sun farfasa motoci, ababen hawa da sauran kayan amfani a fadar sarkin tare da kone
kone - Fusatattun matasan sun kuma kwace sandan sarautar sarkin na Legas da ake kira 'Opa Ase' yayin harin da suka kai
A Larabar nan ne 'yan daba suka yi dafifi a fadar Sarkin Legas, Rilwanu Akiolu da ke yankin Iga Idugaran, a birnin Legas, suka farfasa ababen hawa da sauran kayan amfani da dama kamar yadda The Punch ta ruwaito.
A wani bidiyo da ke yawo a kafafen sadarwa, ya nuna 'yan tawayen sun yi awon gaba da sandar sarautar wadda aka fi sani da 'Opa Ase'.
Wani mazaunin yankin ya shaidawa manema labarai cewa 'yan tawayen da suka cika a fadar, sune dai waɗanda suka cinna wuta a gidan da iyalan gwamna Babajide Sanwo-Olu suke. "Lokacin da suka tafi kai harin gidan mahaifin Sanwo-Olu, yan sanda sun harbi wasu daga cikin su.
Wanda hakan ya fusata su har ta kai sun fara musayar wuta tsakaninsu da ƴan sandan har ta kai sun fi karfin yan sanda. "Yan sandan, wanda ake alakantawa da ofishin 'yan sanda na Adeniji Adele, sun yi gaggawar guduwa daga inda abun ya faru.
"Fusatattun matasan sun nufi hanyar fadar Oba na Lagos. Suna ikirarin cewa shima ma'aikacin gwamnati ne. Maharan suna kai hari ne a duk wani waje mallakin gwamnati," a cewarsa
Source: Legit
0 Response to "'Yan daba sun mamaye fadar Sarkin Legas, sun kwace sandar ikonsa "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?