Yadda dan haya ya kashe mai gidan haya saboda ya hana kawo 'yan mata gida
Thursday, 8 October 2020
Comment
Wani matashi mai shekaru 21 ya halaka mai gidan hayansu mai shekaru 35 a garin Ogidi a jihar Anambra Matashin ya halaka mai gidan ne saboda ya yi yunkurin hana shi kawo mata daban-daban zuwa gidan hayan
Lamarin ya janyo rashin jituwa tsakaninsu kuma dan hayar ya dakko wuka ya daba wa mai gidan hayar wadda hakan ta yi sanadin mutuwarsa Wani dan gidan haya mai shekara 21 Onyemachi Mmaju, ya kashe mai gidan hayar da ya ke zama,
Nonso Oyiboko a garin Ogidi a karamar hukumar Idemili na jihar Anambra. The Punch ta ruwaito cewa an fara samun rashin jituwa tsakanin mai gidan da dan hayan ne bayan Oyiboka ya koka kan yadda Mnaju ke kawo 'yan mata gidan.
Wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta ta ce, "Saboda bai gamsu da hana shi kawo matan da maigidan ke yunkurin yi ba, Mjama ya fito da wuka da kai masa hari, garin hakan ya daba wa Oyiboka wukar a baya.
"Kafin mutane su zo su cece shi, mai gidan ya fadi a kasa jini yana zuba duk jikinsa. An garzaya da shi asibiti inda ya mutu a can. Daga baya 'yan sanda sun zo sun kama Mjama da wasu." Kakakin 'yan sandan jihar, Haruna Mohammed ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce abin ya faru ne misalin karfe 3 na daren ranar Laraba.
"An kawo rahoton zargin kashe wani mai gidan haya, Nonso Umeadi Oyiboka, 35 na garin Ogidi Ani-Etiti a karamar hukumar Idemili North a jihar Anambra da dan hayarsa wani Onyemachi Mmaju, 21, ya kashe shi.
"Bayan rahoton 'yan sandan Ogidi karkashin jagorancin DPO, Ekuri Remigius sun ziyarci wurin inda suka gano wanda abin ya faru da shi kwance cikin jininsa, an kai shi asibitin Iyi Mission Hospital, Ogidi inda likitoci suka tabbatar ya mutu.
An bar gawar a can don bincike," a cewar wani sashi na rahoton kakakin 'yan sandan. Mohammed ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar, John Abang ya bada umurnin a tura binciken zuwa sashin binciken manyan laifuka don zurfafa bincike.
Ya kara da cewa za a gabatar da wanda ake zargin a gaban kotu idan an kammala bincike. Gwamnan da aka zaɓa a karon farko a 2017 yana fatar zarce wa kan mulki idan al'ummar jihar sun dake zabensa a zaɓen da za ayi ranar Asabar 10 ga watan Oktoba.
Source: Legit.ng
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Yadda dan haya ya kashe mai gidan haya saboda ya hana kawo 'yan mata gida"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?