
Wata sabuwa: Ƴan daba sun tarwatsa masu zanga zanga a Kano
Thursday, 15 October 2020
Comment
Wasu da ake zaton yan daba ne sun far ma masu zanga-zanga a jihar Kano - Yan daban sun tarwatsa matasan wadanda suka fito don nuna damuwarsu a kan rashin tsaro a yankin arewacin kasar a daidai titin Kabuga
Sun kuma yi masu sace-sacen wayoyi inda hakan ya sa su hakura da gangamin Rahotanni da muke samu a yanzu, ya nuna cewa wasu yan daba dauke da makamai sun tarwatsa zanga-zangar da wasu matasa ke gudanarwa a jihar Kano.
Matasa a jihar dai sun fito domin yin gangami a kan matsalar tsaro da ake fama da ita a arewacin Najeriya. Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa yan daban sun far wa masu zanga-zangar ne daidai titin kabuga da ke birnin tare da kwace-kwacen wayoyi. Hakan ya tursasa wa masu zanga-zangar hakura da ci gaba da tattakin nasu.
Source: Legit
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Wata sabuwa: Ƴan daba sun tarwatsa masu zanga zanga a Kano "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?