
Turmi da tabarya na kama ta da babban abokina - Magidanci ya sanar da kotu
Ya sanar da yadda matarsa mai suna Zainab take lalata da babban amininsa. Amzat ya bayyana wannan zargin ne bayan Zainab ta sanar da kotun cewa yana farautar rayuwarta domin haka take so a raba aurensu. "Mai shari'a, a gaskiya ni da Zainab muna fada ne saboda halin bin mazanta. Zainab da babban abokina suna fasikanci.
“Ta yi batan dabo na tswon watanni uku inda ta bar gidana. Ta kwashe yarana amma daga bisani sai na gano tana gidan abokina ne kuma amini. "Dumu-dumu na kama su suna faskancin," Amzat yace. Kamar yadda mai karar wacce ta mallaki mashaya ta fara sanar da kotun, ta ce mijinta yana barazanar raba ta da rayuwarta.
Ta zargesa da tozartata tare da zaginta a cikin jama'a da kuma cikin gari. "A koda yaushe yana bibiyar duk inda naje," matar ta sanar. Alkalin kotun, Chief Henry Agbaje, ya shawarci ma'auratan da su tabbatar da ikirarinsu nan gaba a gaban kotun. Ya ce kowannensu ya bayyana da 'yan uwansa biyu a zama na gaba. Ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 2 ga watan Nuwamba.
Source: Legit
0 Response to "Turmi da tabarya na kama ta da babban abokina - Magidanci ya sanar da kotu "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?